Kalmomi Daga Shaykh Fû’âd Az-Zintânî Dangane da JIBWIS
﷽
Tambayar Da Aka Aikawa Shaykh Fû’âd Az-Zintânî, Allâh Ya Kiyaye Shi.
As-Salām ʿalaykum wa raḥmatullāh wa barakātuh.
Zuwa ga Shaykh Fū’ād Az-Zintānī, Allāh ya kiyaye shi, ya shiryar da shi zuwa ga dukkan abin da yake so, kuma ya yarda da shi.
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
A kasarmu Nigeria, muna tare da masu da’awa da suke jingina kansu ga Salafiyyah, kuma suna kiran wannan kungiya tasu Jamāʿah Izālah Al-Bidʿah Wa Iqāmah As-Sunnah (JIBWIS).
*Jamāʿah Izālah Al-Bidʿah Wa Iqāmah As-Sunnah - Ƙungiya Mai Kawarda Bid'ah da Tsayarda Sunnah.
Kuma wadannan mutane suna da wasu abubuwa da ba mu yarda da su ba. Kuma muna fatan Shaykh ya amsa wadannan tambayoyi tare da hujjojinsu daga Al-Qurʾāni da ingantattun Hadisai, tare da fahimtar Magabatan na Ƙwarai.
Cikin Abinda Suke Fada:
1. Suna Kiran malamanmu da Ghulāt at-Tajrīḥ (masu wuce gona da iri wajen suka).
2. Mu’amalarsu da ‘Yan Bidi’a ruwantarwace da rufa-rufa.
3. Sun radawa Salafiyyūn suna na “Madākhilah”.
4. Suna Nasiha ga masu mulki akan Manābir da kuma yanar gizo.
5. Yabonsu a fili ga ‘Yan Bidi’a, irin su Al-Qaraḍāwī, Muḥammad Ḥassān, Safar Al-Ḥawālī, ʿĀʾid Al-Qarnī, Salmān Al-ʿAwdah, Abū Isḥāq Al-Ḥuwaynī, Al-ʿArīfī, Ibn Lādin da sauran su.
6. Za ka same su suna zama tare da As-Ṣūfiyyah (‘Yan Darika) da sauran su.
7. Suna hana dalibansu sauraron kaset na Ash-Shaykh Al-Mujāhid, Rabīʿ bn Hādī Al-Madkhalī, Allāh ya kiyaye shi, ya kula da shi, da sauran malamai.
8. Suna kiran mutane zuwa ga dimokuradiyya da zabe, suna amfani da fatawar Shaykh Muḥammad Nāṣir Ad-Dīn Al-Albānī ga ‘Yan Algeria da ta Shaykh Muḥammad b. Ṣāliḥ Al-ʿUthaymīn (Allāh ya yi musu rahama) a matsayin hujja.
Haka nan, daga keta haddin da suka yi na raba kan Musulmi da shi, akwai:
1. Walāʾ and Barāʾ (Soyayya da Ƙiyayya) a kan qungiyarsu, ba bisa aqida da tafarkin Salafiyyah ba. Kuma cikin misalan haka:
i) Kin amincewar reshe na Jos (jiha a Najeriya) – wadanda suke ƙarƙashin Muḥammad Sānī Yaḥyá Jingir – kowane siga na sallama a cikin Sallah sai sallama guda daya.
ii) Kin amincewar reshe na Kaduna (jiha a Najeriya) – wadanda suka ƙarƙashin ʿAbdullāh Bala Lau – sallama guda daya yayin da suke tabbatar da sauran sigar sallama.
Don haka a kan haka, idan wani daga cikin Limaman masallatansu ya zo da sigar [sallama] da suke qaryata ta, sai su cire shi daga kasancewarsa Limami, ko da kuwa ya kawo musu Hadisan Manzon Allāh (ﷺ) cewa da ya zo da wadannan sigar da suke karyata su.
Don haka, a kan haka ne suka raba jama’a, suka ware Masallatansu. Kuma wanda yake a reshen Jos baya sallah bayan wanda ya ke reshen Kaduna—a mafi yawan lokuta.
iii) Reshen Jos suna aske gemu, sanya tufafin da ke kasa da idon sawu ga maza, da sauke hannu lokacin Sallah—da da’awar cewa daga mazhabar Imām Mālik suka samo haka, Allāh Ya yi masa rahama. Da dai sauran abubuwa da wadannan mutane ke ta keta wa.
Yanzu, tambayarmu, Allāh ya saka muku da alheri, itace:
1. Menene ƙungiya? Kuma menene ƙungiyanci? Kuma yaushe aka cewa wane Hizbi ne? Kuma shin duk wanda ya shiga daya daga cikin wadannan kungiyoyi ya zama dan bidi’a kuma za'a mu’amalanceshi a matsayin dan bidi’a?
2. Menene nasihar ku ta As-Salafiyyūn, ga wadannan mutane gaba daya, da kuma daliban ilimi a kebance.
3. Shin kuna bani shawara ni da ragowar daliban ilimi da mu shiga wannan ƙungiya?
4. Shin za’a dau wannan kungiyar a matsayin ‘Yan Bidi’ah?
5. Suna cewa: “Yaya ba za mu karanta littafan Sayyid Quṭb, Al-Qaraḍāwī, Muḥammad Ḥassān, da wasunsu daga
Cikin ‘Yan Bidi’ah ba, alhali kuwa kuna karanta littafan As-Suyūṭī, Ibn Ḥajar, An-Nawawī, da kuma sauran su da wasunsu cikin manyan malamai”. Ta yaya za mu yi raddin wannan shubuhar?
6. Menene Al-Muwāzanāt? Shin Salaf suna auna ayyukan Yan Bidi’ah mai-kyau da mara kyau?
7. Shin ya dace daliban Salafiyyah a Nigeria su yi shiru game da irin wannan lamari?
8. Menene fahimta ta daidai ta Salafiyyah a wurinku? Kuma yaushe aka cewa wane da wane Salafawa ne?
Kuma muna fata Shaykh zai bamu amsar ko ta hanyar sauti ne – kuma mun fi son sauti, domin mu yaɗa shi a Najeriya.
Muna godiya sosai a gare ku.
Martanin Shaykh Fû’âd Az-Zintânî, Allâh Ya Kiyaye Shi.
Wa ‘Alaykum as-Salām wa Raḥmatullāh wa Barakātuh. Ḥayyāk-Allāh ya dan‘uwanmu ‘Abdur-Raḥmān.
Dangane da tambayarka akan wadanda suka kira kansu da: Jama‘ah Izālah Al-Bid‘ah Wa Iqqāmah As-Sunnah (Ƙungiya Mai Kawarda Bid'ah da Tsayarda Sunnah)- (JIBWIS). Kuma ka ambaci wasu daga cikin kalamansu (da ayyukansu); Suna Kiran manyan malamai na Sunnah da Ghulāt at-Tajrīḥ (masu zurfafawa a yin suka), kuma su (JIBWIS) suna bada kariya ga ‘Yan Bidi’ah (Mudāhanah), kamar yanda kuma suna jifan Salafawa da sunan “Madākhilah”, kuma suna yin nasiha ga shuwagabanni a saman minbarori a fili, kuma suna yin yabo ga ‘Yan Bidi’ah irinsu: Qaraḍāwī, da Muḥammad Ḥassān, da Safar Al-Ḥawālī, da ‘Ā’idh Al-Qarnī, da Al-Ḥuwaynī da Al-‘Arīfī da ibn Lādin da wasunsu. Haka kuma, suna zama da ‘Yan Bidi’ah (‘Yan Dariƙu/ As-Ṣūfiyyah), kamar yanda kuma suna tsoratarda dalibansu daga sauraren sautukan Shaykh Rabī‘, Allāh ya kiyaye shi, da waninsa daga cikin malamai. Haka kuma, suna kira zuwa ga dimukradiyyah da yin zabe. Haka kuma suna ƙulla soyayya da qiyayya akan ƙungiyarsu. Kuma, ka kawo misalai akan wannan da abunda ya faru: ga ƙungiyar reshen Jos basa tabbatarda sallama a sallah sai guda daya tak, haka su kuma reshen Kaduna na qungiyar basa tabbatar da sallama guda daya a sallah. Abisa wannan da wani limami zai zo da wannan sigar (a masallacinsu) zasu cire shi (daga limanci), kuma basa karbar hadisai ingantattu akan hakan.
Haka kuma, suna aikata wasu ayyukan sabo kamar aske gemu, da sakin tufafi (zuwa qasa ga idon sau).
Zance, Allāh yayi maka albarka, wannan kungiya a hakikanin gaskiya kari ne ga ƙungiyar Ikhwān-ul-Muslimin idan suna fadin maganganu da ka ambata akansu. Kuma wannan ƙungiyar bata bakin komai acikin Salafiyyah (tafarkin Magabata na Kwarai). Kasantuwar suna kiran kansu da Ƙungiya Mai Kawar da Bidi’ah da Tsayarda Sunnah. A’a, su dai ƙungiya ce Ta Kawar da Sunnah da Tsayarda Bidi’ah. Kuma, basu san Sunnar ba! Domin da sun san Sunnah da basu yi ƙungiyanci ba, wannan bangarancin da ƙulla soyayya da ƙiyayya akansa akan ƙungiyarsu.
Amma tambayarka gameda ƙungiya da ƙungiyanci: menene su kuma yaushe za’a ce wane Ḥizbī ne (dan ƙungiya), ko kuwa duk wanda ya shiga wata ƙungiya ya zamo dan Bid’ah kuma za’a yi masa mu’alamalar ‘Yan Bidi’ah?
Zance maka Ḥizbiyyah (ƙungiyanci) shi ne soyayya ƙuntatacciya, gina so da ƙi akan ƙungiya akan wata Jama’a; a ƙulla ƙauna da gaba akan wannan duk wanda ya dace da ƙungiyarsu zasu so shi wanda kuma ya barranta daga wannan ƙungiyar tasu zasu barranta da shi kuma su ƙi shi. Wannan shi ne ƙungiyanci!
Wanda ya shiga cikin wannan ƙungiyar kuma yasan halinsu to yana cikinsu! Za’a hada shi tare dasu kuma za’a yi masa mu'amala irinta ‘Yan Bidi’ah, saboda ƙungiyanci Bidi’ah ce.
Menene nasiha ta gaba daya ga wadannan mutane?
Suji tsoron Allāh, kuma su daina wannan ƙungiyancin! Kuma, su tuba zuwa ga Allāh daga sukar da sukeyi ga malamai da tuhumarsu ga Salafawa tuhumomi na ƙarya! Kuma, su gyara kurakuransu bayyanannu a fili!
Amma nasihata zuwa ga Salafawa, da daliban ilmi da suka shiga wannan ƙungiyar wajibi shi ne su barranta daga wannan ƙungiyar da tsoratarwa akanta da neman su tuba zuwa ga Allāh (Subḥānahu wa Ta’alā). Wajibin Salafawa ne su kasance a ware daga irin wadannan. Cewar shin za’a dauke su a matsayin ‘Yan Bidia; eh, tabbas in har wadannan zantuttukansu ne. Kuma sun samo asali daga Ikhwān-ul-Muslimīn. Allāh yayi maka albarka.
Kuma abunda ke ƙarfafar wannan cewarsu ta yaya ba zamu karanta litattafan Sayyid Quṭub da (Yūsuf) Al-Qaraḍāwī da Muḥammad Ḥassan ba, suna ƙiyasta wannan da karanta littafan Suyūṭī, da Ibn Hajar, da An-Nawwawī.
Sai muce musu: “yaku jahilai, ina za’a hada tsakanin ƙasa da sama?” Ina za’a kwatanta, wadannan ‘Yan ƙungiya, da wadannan malamai da manufarsu ita ce taimakon Sunnah, kuma basa bangaranci ga wani?
Manufarsu kawai ita ce taimakawa Sunnah, sunyi kuskure acikin wasu al-amura kuma kuskurensu abun yafewa ne. Ba a ƙiyasta su da wadancan!
Wadannan mutanen da ka ambata sunayensu, su ne masu kira zuwa ga Bid’ah! Don haka, kuskure ne a kwatanta Al-Qaraḍāwī da As-Suyūṭī, Ibn Hajar, ko An-Nawawī. Akwai banbanci mai yawatsakanin guda biyun. Wannan shubuha ce da aka rushe tsawon zamani kafin yanzu. Wadannan malamai namu kamar Suyūṭī, da Ibn Ḥajar, da Nawwawī manufarsu itace taimakon Sunnah, suna da wasu kura-kurai kuma basuyi bangaranci ba. Amma su wadannan sunyi bangaranci kuma sun wayi gari ‘Yan Bid’ah, saboda haka su ana ƙiyasin su ne da jagororin ‘Yan Bid’ah wadanda suka kasance akan ƙungiyoyi na bata kamar su: Wāṣil dan ‘Aṭā', da An-Naẓẓām, da Jahm (dan Ṣafwān) da Abū Manṣur al-Māturīdī da ire-irensu. Wadanda ka ambata ana kwatanta su ne da wadannan. Kuma, ku duba matsayar malamai gameda su (Al-Qarḍāwī da irinsu).
Kuma, ka duba matsayar malamai gameda al-Karabisi lokacin da yace -furucina-: “da al-Qurʾāni halitta ne”, tareda tarin ilimi da yake dashi. Kuma, fatawa tana zuwa ta dawo kansa amma, Imām Aḥmad ya tsoratar da mutane akansa, kuma yayi magana akansa. Kuma, bamu san wanda suka zo bayan Imām Aḥmad ba (daga cikin malamai) da yace ta yaya za’a tsoratar daga Al-Karabīsī amma baku tsoratarwa kan wane da wane. Haka ma shi Al-Karabīsī a lokacinsa ya rubuta wani littafi da ya tattara kura-kuran malaman hadisi aciki yace: “suma sunyi kuskure”. Sai Imām Aḥmad yace: “wannan ya tattarawa ‘Yan Bid’ah abunda basu iya tattarawa ba”. Don haka wannan shubuha ce rusassa.
Amma tambayarka gameda muwazana kuma ko Magabata sun kasance sunayin muwazana ga ayyukan ‘Yan Bid’ah da bata da suka gabata? Ita bid’ar muwazana ita ce abunda ‘Yan Surūriyyah da Quṭūbiyyūn suke ambatawa cewa; idan kayi magana ko zakayi magana akan wani, dole ka ambaci kyawawan ayyukansa tareda munanan ayyukansa. Ka auna tsakanin wannan da wannan. Kace Sayyid ƙuɗub misali yayi suka ga Mu’awiya (Raḍī-Allāh-‘Anhumā) saidai yana da ƙoƙari yana da ilimi ka ambaci abunda Allāh Yaso na kyawawansa. Kada ka taqaita ga ambaton abunda aka kamashi da su na kura-kurai kawai. Wannan ba hanyar Magabata ba ce! Magabata sun kasance sunayin magana akan mutum su ambaci karkatarsa kuma basa ambaton wani abu na kyawawansa. Eh, idan ana tarihin mutum suna ambaton kyawawansa da munanansa. Amma idan ana son a tsoratar gameda shi ba’a ambaton kyawawan ayyukansa suna ambaton abunda aka kama shi da shi ne kawai. Da zamu ambaci kyawawan toh, mecece fa’idar tsoratarwa garesa?!
Ko yana halasta daliban ilimi Salafawa a Najeriya suyi shiru acikin irin wannan ƙadiyyah. Sai muce musu kuyi inkari da gwargwadon ƙarfinku, kada kuyi shiru. Ku bayyana ingantacciyar Salafiyyah abisa ma'anarta ingantacciya kada kubar wadannan su maƙale a bayanku suna nuna cewa suna kan Salafiyyah kuma ba haka suke ba. Salafiyyah ita ce al-Qurani da Sunnah abisa fahimtar Magabata, ginshiƙen manhajin Magabata sanannu ne, kuma ginshiƙen Sunnah sanannu ne. Wanda ya sabawa wadannan ginshiƙen shi dan Bid’ah ne batacce, wanda ya sabawa ginshiƙi daya daga cikin su shi dan Bid’ah ne batacce! Wanda kuma yayi riƙo da ginshiƙen Sunnah toh shi Salafī ne.
Saboda haka ya kamata ga daliban ilimi acan (Najeriya) da su bayyanawa mutane haqiqanin Salafiyyah cikin: ilimi, da haquri, da hikimah. Kuma, su kira mutane zuwa ga aiki da al-Qurani da Sunnah bisa fahimtar Magabata na ƙwarai. Su saka girmama tafarkin Magabata acikin zuƙatan mutane suyi takatsantsan akan masu Da'awa na wannan zamani daga cikin Ḥizbiyyūn da wasunsu.
Allāh, Subḥānah wa Ta‘alá, muke roqo da ya datar damu duka. Kuma, ya shiryar da batattun Musulmi, kuma Ya taimaki Da'awar Salafiyyah a ƙasarku (Najeriya).
Allāh Ya ƙara tsira da aminci ga Annabinmu Muḥammad da iyalansa da Sahabbansa.
Abū Sulaymān (Shaykh Fū'ād Az-Zintānī - Allāh Ya kiyaye shi) ne ya fada a ranar: 13, ga watan Sha’bān, 1444 bayan Hijira.
Allāh ne masani.
[Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial]