Menene as-Salafiyyah?
Salaf su ne Magabata na Kwarai. Duk wanda ya bi tafarkinsu kuma ya ci gaba akan hanyar su shine salafi.
Al-Imâm ʿAbdur-Rahmân al- ʿAwzâʻî (رحمة الله عليه) ya ce:
"A gareku ruwayoyin Salaf, ko da mutane sun yarda ku. Kuma ku nisanci ra'ayoyin mutane koda kuwa an gyara su da magana mai dadi."
(Sharh Usul itigad Ahlis-Sunnah wal Jama'ah na Al-Lalikai 1/147)
Don haka Salaf sune Sahabban Mazon Allâh; Muhammad (ﷺ) da wadanda suka bi su tun daga zamanin farko!
Amfani da kalmar Salaf ya yadu a tsakanin Musulmin farko kuma an yi amfani da shi don jagorantar mutane zuwa cikin Minhaj (Hanya) na Sahabah da wad’anda suka bi su.
Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Fatimah (رضي الله عنها) a kan gadon mutuwarsa:
"Ku ji tsoron Allaah kuma ku yi haquri domin lallai ni Salaf ne mai albarka". Watau Magabaci mai albarka!"
(Sahih Muslim 2450 )
Mazon Allâh (ﷺ) ya ce:
"Bani Isra'ila sun kasu kashi saba' in da biyu kuma Al'ummata za ta kasu kashi saba'in da uku. Dukkan su suna cikin wuta sai dai wata kungiya". Suka ce: "Kuma wace mazhaba ce ya Manzon Allâh?" Ya ce: "Abin da nake a kai da Sahabbaina."
(At-Tirmidhi #2542 / Hassan; Shaykh Al-Albaani رحمة الله عليه )
Al-ʿAllãmah Ash-Shaykh Muhammad b. Sãlih Al-ʿUthaymin (رحمة الله عليه رحمة واسعة) - Su Wanene Salaf?
Al-ʿAllãmah Ash-Shaykh Sãlih b. Fawzãn Al-Fawzãn - حفظه الله
Manhajin Magabaata na Kwarai ya daace da kowanne zamani, kuma wanda yayi inkarin hakan yayi kuskure babba.