Ɓoyayyiyar Shirka
Mazon Allãh (ﷺ) yace: Ɓoyayyiyar Shirka: mutum ya tsaya sallah sai ya ƙawata sallarshi domin ya ga wani mutum na kallonshi.
Ire-Iren Shirka: Shirka Ƙarama
Ita ce wadda aka kira Shirka a Qur'ãni ko Sunnah, amma wadda ba ta cikin jinsin Shirka Babba. Misali, aikata wasu ayyuka domin Riya (don a gani a yaba ba don Allãh shi kaɗai ba), rantsuwa da wannin Allãh, cewa "abunda Allãh ya so kuma abunda abunda wane-da-wane ya so" da sauransu.
Ire-Iren Shirka: Shirka Babba
Lallai wanda ya sanya wa Allâh kishiya wajen bauta Allâh ya haramta mishi Aljannah kuma makomarsa wuta. Kuma ga azzalumai basuda mataimaka. [Sûrah Al-Mâ’idah : 72].
Daga Hadarurrukan Shirka
….Lallai, duk wanda ya sanya wa Allāh kishiya wajen bauta Allâh ya haramta mishi Al-Jannah kuma makomarsa wutâ. Kuma ga az-Zalumai (masu Shirka da masu aikata laifi) babu mataimakâ. [Al Mâʾidah:72]