Wasiyya Ta Ga Waɗanda Suke Ƙoƙartawa Wajen Riko Da Littafin Allãh
﷽
Alhamdulillãh (Dukkan yabo ya tabbata ga Allãh shi kaɗai), kuma ina yi wa Manzon Allãh (ﷺ) salaati, da ahlinsa da Sahabbansa, bayan haka.
Wasiyya ta ga waɗanda suke ƙoƙartawa wajen riko da littafin Allãh da sunnar Manzon Allâh (ﷺ) da kuma tafarkin Magabaata shi ne ku yi hakuri. Wallāhi, lokaci kaɗan ya rage kafin taimakon Allâh ya zo. Manzon Allâh (ﷺ) ya sanar damu cewa:
بَدَأَ الإِسْلاَمُ غَرِيبًا وَسَيَعُودُ غَرِيبًا فَطُوبَى لِلْغُرَبَاءِ
“Musulunci ya fara a matsayin abu baaƙo kuma zai koma zama abu baaƙo domin haka yi bushara ta ɗûbâ (wata bishiya a aljannah) ga baaƙi (Al-Ghurabã)” (1)
Idan da za ka karanta lãbãran Annabãwa da Manzanni, Musamman tarihin Manzon Allãh (ﷺ) kuma da zaka ga zaluncin da suka fuskanta yayin dasuke Makkah, Wallãhi zaka fahimci cewar garemu ne yin hakuri yayin fuskantar jarrabãwa da ibtila'i. Abubuwa sun tsananta matuƙa ga masu imaani kuma jurewa bai kasance da sauki ba. Hasali ma, wasu Musulmai daga farko-farkon kwānakin Musulunci an kashe su saboda imãninsu, wannan ne ya sanya Sumayyah (Allâh ya kara mata yarda) ta kasance Shahidiya ta farko a Musulunci. Domin haka sadaukarwar da Musulman farko sukayi muke amfanuwa a yau! Manzon Allãh ya fuskanci zalunci, da matsaloli a lokacinsa, kuma ya sanar da Sahabbai cewa Addinin zai koma baaƙo kamar yanda ya kasance a da. Domin haka albishir ga baaƙi!
Su wanene baaƙī? Ibn Rajab Al-Hanbali (رحمه الله) ya fadi a Kashf-ul-Kurbah fî wasfi Hãli Ahlil-Ghurbah; inda yayi bayaanin rewayoyi dasuke magana akan baaƙī (wato Al-Ghuraba), cewar daga cikin rewayoyin, baaƙī sune waɗanda zasu kasance salihai kuma zasu yi kokarin zama shiryayyu yayin da mutane da yawa suka ɗauki hanyar da ta sãɓãwa shiriya. Domin haka, yayin da saura suke juya baya daga addinin Allãh su zasu cigaba da yin riko da Addini. Yaayin da wasu suke yaaƙar sunnar Manzon Allãh (ﷺ), su baaƙī (Al-Ghurabã) zasu farfado su kuma rayar da Sunnah! Domin haka garemu ne yin hakuri!
Abu na biyu, mu sani cewar bazamu zamanto muminai na haƙiƙa ba faace Allãh ya jarraba da’awar da muke (ta imani)! Allãh ya fadi:
الٓمٓ - أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتْرَكُوٓا۟ أَن يَقُولُوٓا۟ ءَامَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ
Alif-Lâm-Mîm. Shin mutane sunyi tsammanin cewa za a bar su domin sun ce; “munyi imaani”, kuma ba za a gwada su ba. (2)
Saboda haka shin zai iya yiwuwa ka zamanto mumini kuma baza’a jarraba ka ba?
وَلَقَدْ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَلَيَعْلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُوا۟ وَلَيَعْلَمَنَّ ٱلْكَـٰذِبِينَ
Kuma tabbas mun jarrabi waɗanda suka zo gabaaninsu. Kuma lallai Allâh zaii bayyana (gaskiyar) waɗanda suke masu gaskiya kuma lallai zai bayyana (ƙaryar) waɗada suke makaryata, (duk da cewar Allāh ya sani tun kaafin ya gwada su). (3)
Saboda haka, ta hanyar jarabawoyi da fitintinu, Allãh yana bayyana waɗanda suke muminai na haƙiƙa, ya kan kuma fallasa waɗanda kawai suke da’awar hakan (cewa su muminai ne a gaskiya). Mutane da yawa suna da’awa; “muna kamanta sunnah.” “Muna raaya sunnah,”, “Muna kokari akan Addini”, amma yayin da waɗannan suka fuskanci ƙãlubale daya ko biyu sai su gudu, wato su juya baaya daga addinin Allãh! Allãh (ﷻ) yace:
وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّىٰ نَعْلَمَ ٱلْمُجَـٰهِدِينَ مِنكُمْ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَنَبْلُوَا۟ أَخْبَارَكُمْ
Kuma tabbas, zamu gwada ku har sai mun jarraba waɗanda suke kokartawa (a hanyar Allāh) da kuma As-Sâbirûn (masu hakuri), kuma zamu gwada akhbārakum (waato wanda yake makaryaci dakuma wanda yake da gaskiya). (4)
Manzon Allãh (ﷺ) ya tunatatar da Sahabbai yayin da suka kawo masa kukan wahalhalun dasuke fuskanta wajen kafirai, (ya tunatar dasu cewar) har me suka fuskanta?! Sanda waɗanda suka zo kafinsu za a ce wa ɗayansu “ko ka ajiye imaninka (wato ka kafirta) ko ka shiga wannan wutar”, kuma sai su zabi wuta sama da rabuwa da imaaninsu.
Yi nazari akan ƙissar Ashãb Al-Ukhdûd (Mutanen raami) a Sûratul Burûj:
إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌۭ - وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌۭ - وَمَا نَقَمُوا۟ مِنْهُمْ إِلَّآ أَن يُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ
Yayin da suka zauna gefen ta (wuta), kuma suka shedi abunda suke aikatawa muminai (waato ƙona su). Kuma basuda wani laifi faace cewar sunyi imani da Allãh, Mafi Girma, Mai cancantar dukkanin yabo! (5)
Yi tunani, haka muminai suka zauna gefen wuta, sojojin suna kiransu daya bayan daya, sai a tambayesu “zaka ajiye addininka ko ka shiga wuta.” Wasu sun bar imaaninsu domin basa son su mutu…amma suna raaye a yau? Wallāhi sun mutu.
Da ace sun tsaya kan Addinin Allāh da sun kasance matattu a yanzu amma rayayyu cikin ni’ima mai wanzuwa daga Allãh. Haka zalika wasu suka tsaya suka tabbatu! Yayin da Manzon Allãh (ﷺ) ya bada laabarin wannan aukuwa ya ambaci cewar akwai wata mace wadda take rike da jinjiri a tare da ita, yayin da lokancinta yazo na yanke hukunci sai ta kalli jinjirin- tana tunani; shin ta shiga wuta duk da wannan jinjirin?- na ranste da Allãh kwatsam jinjirinnan sai yayi magana! Jinjirin ya cewa mahaifiyarshi ta shiga wuta! Yi tunanin jinjiri ya cewa mahaifiyarshi ta shiga wuta, sai suka shiga kuma suka mutu domin wannan imaanin!
Abu na uku, mu sani cewar imaaninmu shi ne mafi tsaadar abunda muka mallaka, domin haka bazamu yarda mu rasa shi domin Duniya, ko cimma mukamai, ko yardar wani ba! Tsadar Addinin ta wuce a rasa shi domin komai! Meyasa? Saboda shigarmu aljannah ko wuta ya dogara ne akan addinin. Idan imaninka ya tsayu, ko da ka fito daga gida wanda yake na talauci ko kuma kunci zaka kasance cikin masu nasara! Amma idan kanada gazawa a imaninka kokuma imaninka na da tawaya ko da ka fito daga gidan dukiya da matsayi da shahara mukaminka cikin al’umma ba zai taimakeka ko ya amfaneka ba! Manzon Allãh (ﷺ) yace:
وَمَنْ أَبَطْأَ بِهِ عَمَلُهُ لَمْ يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ
Kuma duk wanda ayyukanshi suka makarar da shi tsatsonshi ba zai ƙaddamar da shi ba (waato bazai kara masa sauri ba). (6)
Domin haka ina yi muku nasiha da ku tsaya ku tabbatu akan Addinin ku kuma ku dage wajen kaucewa sãsantawa (game da addiniku, sadaukar da sashen shi don wani abu ko fifita wani Abu sama da shi), sãsantawa ba ya halatta, faace a halin tsananin da ya kai makura inda aka tilasta. Zamu bayyana addininmu ne, wannan shi ne abunda muke kai, kuma shi ne gaskiya. Muna rokon Allãh ya sanya mu daga cikin baaƙi (Al-Ghurabã), kuma ya saukaka mana al'amuran mu.
Kuma Allãh ne masani.
Abû Kawthar Luqmãn b. ʿAbdir-Ra'ûf (وفقه الله)
24/ November/ 2021.
Bayanin Kula
(1) - Sahih Muslim 145
(2) - Sûrah Al-ʿAnkabût : 1 - 2
(3) - Sûrah Al-ʿAnkabût : 3
(4) - Sûrah Muhammad : 31
(5) Sûrah Al-Burûj : 6 - 8
(6) - Sahih Muslim 2699