Jin Kunyar Allãh
﷽
Al-Allãmah Rabî ʾ b. Hãdî Al-Madkhali (Allãh ya Kara mishi Nisan kwana) yace:
"Dole ne mu ji kunyar Allãh a Duniyar nan da kuma lahira (ta hanyar aikata abunda ya yi umarni da shi da kuma gujewa abunda yayi hani da shi a rayuwar nan da kuma jin kunyar haduwa dashi a halin saba mishi). Wallãhi babu wanda yake saba wa Allãh kuma yake zalunci face babu kunya a tareda shi ko kunya ta mishi karanci.
Kunya lamari ne me girma, kuma daga cikin ribar shi shine yana iya kasancewa mutun yayi niyyar aikata zunubi har ya kusance sa se ya tuna yace : "hakika Ubangiji na yana kallo kuma yana ji na"; se mutum ya ji kunya da tsoro a lokacin. Saboda haka, wannan kunyar da tsoro sai ya karkataka daga aikata wannan zunubin.
Kunya na daga cikin abubuwa masu girma wanda ke sa kamewa (daga sabo) - kunya da tsoron Allãh tareda Imãnin gaskiya. Don haka, wajibi ne a garemu mu karfafa Imãnin mu (yarda da Ubangiji) kuma mu saka kunya a zukatanmu ta hanyan karanta tarihin annabawa (tsira da amincin Allãh ya tabbata a garesu).
Daga Al-Majmû - Bayanin ʿAqîdah Na Salaf (Vol. 2/ Shaf. 146).
Wanda Ya Wallafa Littafin: As-Sãbûnî.
Daga Tashar Telegram Ta Al-Allãmah Rabî ʾ b. Hãdî Al-Madkhali - حفظه الله.
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Fassarar Salafi Centre Nigeria.