Kar Ka Biyewa Sha’awarka - Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. Bâz

Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. ʿAbdillâh bin Bâz yace;

Kuma duk wanda ya juya baya wa Qurʾâni da Sunnah mabiyin son ranshi ne, kuma mai kangerewa Unbangijinsa ne, kuma mai cancantar a ƙyamata ne da kuma azâbâ. Kamar yanda Shi- Mafi ɗaukaka- yace:

فَإِن لَّمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَكَ فَٱعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَآءَهُمْ ۚ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيْرِ هُدًى مِّنَ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Amma idan basu amsaka ba (waato basu yi imâni da tawhîdî ba kuma basu bi ka ba), toh ka sani cewa kaɗai suna bin sha’awoyinsu ne, kuma wa ya fi ɓata sama da wanda ya bi sha’awoyinsa ba taare da shiriya daga Allāh ba?

Sûrah Al-Qasas:50

Shi, Mafi ɗaukaka- yace a siffantawarsa ga kaafirai:

إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهْوَى ٱلْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلْهُدَىٰٓ

Kaɗai suna bin zaato ne da abunda kawunansu suke sha’awâ, alhanin tabbas shiriya ta zo musu daga Ubangijinsu

Sûrah an-Najm:23 

Biyewa son rai-kuma wurin Allâh muke neman tsari- na kashe hasken zuciya, kuma yana tokare (cimmawa) zuwa ga gaskiya. Kamar yanda Shi- Mafi ɗaukaka- ya ce;

وَلَا تَتَّبِعِ ٱلْهَوَىٰ فَيُضِلَّكَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَضِلُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ

Kuma kar da ka bi son rai domin zai ɓatar dakai daga hanyar Allâh

Sûrah Sâd: 26

Domin haka yi hattarâ- Allâh yayi maka Rahama- daga bibiyar son rai da kuma juya baaya daga shiriya. Kuma gareka shi ne yin riƙo da gaskiya, yin kira zuwa gareta, dakuma yin tâkâtsantsan daga duk wanda ya sâɓâ mata, domin ka cimma alherin wannan duniyar da kuma Laahira.

[ Daga: Majmûʾ Al-Fatâwâ (2/ 149-150) | Fassarar Turancin Abû ʿAffân ʿAbdul-Qâdir Al-Kowsî | Fassarar Hausa AMMAN CIRCLE Editorial]

Previous
Previous

Kyakkyawar Mu’amala da Mutane