Kyakkyawar Mu’amala da Mutane
﷽
Imãm ibn Rajab - رحمه الله - (wanda ya rasu a shekara 795H.) ya ce;
Fadin Shi [Annabi Muhammad ﷺ]:
Kuma ka mu'amalanci mutane da kyakkyawar ɗabi’a (Tirmidhî)
Wannan [kyautata mu’amala da wasu] yana daga cikin rassan Taqawa, kuma taqawa bata cika ba tare da shi ba. haƙiƙa shi [Annabi Muhammad ﷺ] ya ambaci hakan musamman domin buƙatuwar bayaanin (a kan wannan).
Tabbas, da yawa sun (kuskure) wajen tsammanin cewar taqwã kaɗai ta taƙaita ne a bada haƙƙin Allāh, ba (tare da) [bayar] da haƙƙin wasu ba.
Daga: Jãmi’ Al-'Uloom Wal-Hikam
Fassarar Amman Circle Editorial daga Ustãdh Mustafa George
6 Rabiʾ Ath-Thãni 1444 هـ
1 November 2022.