Kurakurai Cikin Aqeeda - Gina Masallatai Saman Kaburbura, Yin Sallah A Wurin Da Gina Rufi Akan Su - Shaykh ʿAdul-ʿAzîz bn Bâz
﷽
2.) Gina Masallatai Saman Kaburbura, Yin Sallah A Wurin Da Gina Rufi Akan Su.
Duka waɗannan na daga abubuwan da ke kaiwa zuwa ga Shirka (sanya wa Allâh abokan tarayya a bauta). Kuma Annabi (ﷺ) ya la'anci yahudawa da nasara saboda wannan. Kuma ya yi gargadi akan Shi, yana mai cewa:
"La'anar Allâh ta tabbata akan yahudawa da nasara, sun riki kaburburan annabawansu a matsayin wuraren bauta."
Muttafqun ʿAlaihi (Bukhârî da Muslim)
Kuma ya ce:
"Ku saurara! Haƙiƙa waɗanda suka zo gabaninku sun kasance suna ɗaukan kaburburan annabawansu da salihan cikinsu a matsayin wuraren bauta. Ku saurara! kar da ku dauki kaburbura a matsayin wuraren bauta, Lallai na hane ku da aikata haka."
Muslim ya Rawaito a Sahihinsa daga Hadisin Jundab.
Kuma Muslim ya rawaito a Sahîh, daga Jabir bn ʿAbdillâh Al-Ansârî, Allâh ya yarda da shi, wanda ya ce:
"Manzon Allâh (ﷺ) ya haramta sumunce kabari, zama a kanshi, da yin gini a kanshi."
Kuma akwai hadisai dayawa da wannan ma'anar.
Abunda ya zama wajibi akan Musulmai shi ne yin hattara da wannan, da yi wa juna wasiya da barin wannan, saboda gargadin (da) Manzon Allâh (yayi) game da wannan. Saboda yana daga hanyoyin da ke kaiwa zuwa sanya na cikin kabari a matsayin abokan tarayya da Allâh, yin kira (neman taimako, addu'a) zuwa garesu da neman agaji da tallafi daga wurinsu, da sauran nau'o'in Shirka.
Sannan Abu ne sananne cewa Shirka ita ce mafi girma, mafi hadarin zunubi. Don haka wajibi ne ayi hattara da ita da abunda zai kai zuwa gareta.
Sannan Allâh ya yi wa bayinSa kashedi game da ita a ayoyi da dama: daga cikinsu shi ne fadinsa, Mafi ɗaukaka:
﴾إِنَّ اللّهَ لاَ يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَن يَشَاء﴿
"Haƙiƙa Allâh ba ya yafewa sanya mishi kishiya wajen bauta amma yana yafewa koma bayan haka ga wanda ya so"
Sûrah An-Nisâ' (48)
Da fadinSa, Mafi ɗaukaka:
﴾وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ﴿
"Kuma haƙiƙa an yi wahayi gareka da waɗanda suka zo gabaaninka (cewa): "idan ka aikata Shirka, lallai ayyukanka zasu lalace kuma za ka kasance cikin asararru."
Sûrah Az-Zumar (65)
FadinShi, Mafi ɗaukaka:
﴾وَلَوْ أَشْرَكُواْ لَحَبِطَ عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَعْمَلُونَ﴿
"Kuma da sun aikata shirka, da abunda suka kasance suna aikatawa ya rushe musu (ba zai amfane su ba)".
Sûrah Al-An'âm (88)
Kuma akwai ayoyi da yawa da wannan ma'anar.
Daga: Kurakurai cikin Aqeeda na Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. Bâz (رحمة الله عليه رحمة واسعة)
Daga Fassarar Abû ʿAffân ʿAbdulQâdir Al-Kowsî - وفقه الله.