Kurakurai Cikin Aqeeda - Musanta (ƙaryata) ʿUluww na Allâh da Istiwa - Shaykh ʿAdul-ʿAzîz bn Bâz
﷽
Muqadimah:
Daga Abdul ʿAzîz bn ʿAbdillâh Bn Bâz zuwa ga duk wanda ya gani daga Musulmai. Allâh ya daatar da su zuwa ga abunda ya ƙunshi yardar Sa, kuma Ya ƙara musu ilimi da Imâni, Âmîn.
As-Salâmu ʿalaikum wa Rahmatullâhy wa Barakâtuhu. Bayan Haka:
Ya iso gareni cewa dayawan Musulmai suna fadawa cikin kurakurai a aqeeda da abubuwan da suke tunanin cewa (daga) Sunnah su ke alhalin kuwa bidi'o'i ne. Daga cikinsu:
1.) Musanta (ƙaryata) ʿUluww na Allâh (kasancewar Allâh a sama da halittunSa, a zaatinSa) [1] da Istiwa [2] na Allâh Saman Al'arshinsa
Abu ne sananne cewa Allâh - Mafi Girma da ɗaukaka- Yayi bayaanin wannan a LittafinSa Mai Daraja (Al-Qurʾân), inda Shi - Mafi ɗaukaka- ya ce:
﴾إِنَّ رَبَّكُمُ اللّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ﴿
Haƙiƙa Mahaliccinku shi ne Allâh, Wanda Ya halicci sammai da kasa a Kwana Shida, sannan ya daidaita saman al'arshinSa (ta hanyar da ta daace da MulkinSa).
Sûrah Al-A'râf (54)
Ya ambaci wannan [wato daidaituwarShi saman al'arshinSa] a wurare bakwai a LittafinSa Mai Girma, wanda ya haɗa harda wannan ayar. [3]
Kuma yayin da aka tambayi (Imâm) Mâlik, Allâh yayi mishi rahama, game da wannan, ya ce: "Al-Istiwa abu ne sananne, kayfiyarshi (wato haƙiƙanin siffar, ta yaya ya ke) abu ne wanda ba a sani ba, kuma yin imani da shi waajibi ne." Kuma wannan shi ne abunda saura daga cikin As-Salaf (Magabaata) suka fadi.
Kuma ma'anar "Al-Istiwa Abu ne sananne": yana nufin a Larabci. Kuma ma'anar kalmar shi ne 'zamantowa a sama da (da abubuwa)' da kuma 'nufar sama'.
Kuma Shi - Mafi ɗaukaka - ya ce:
﴾فَالْحُكْمُ لِلَّهِ الْعَلِيِّ الْكَبِيرِ﴿
Hukunci ga Allâh yake Shi kaɗai, Mafi ɗaukaka (Al-ʿAliyy) Mafi Girma (Al-Kabîr)
Sûrah Al-Ghâfir (12)
Kuma Shi - Mafi ɗaukaka - ya ce:
﴾وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴿
Kuma kiyaye su ba ya gajiyar da Shi, kuma Shi ne Mafi ɗaukaka (Al-ʿAliyy), Mafi Girma (Al-Adhîm)
Sûrah Al-Baqarah (255)
Kuma Shi - Mafi ɗaukaka - ya ce:
﴾وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴿
Gareshi dukkanin kalamai kyawawa ke hawa…
Sûrah Al-Fâtir (10)
[Ya tabbatar da wannan] a ayoyi da dama waɗanda suke nuni ga ɗaukakarShi da kasancewar Shi saman komai (a zatinShi), da cewar Shi -Mafi ɗaukaka - yana saman Al-'arshinSa saman dukkanin halittu.
Kuma wannan shi ne kalaamin Ahl-us-Sunnah wal-Jamaʾah daga Sahabban Annabi (ﷺ) da wasunsu.
Daga: Kurakurai cikin Aqeeda na Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. Bâz (رحمة الله عليه رحمة واسعة)
Daga Fassarar Abû ʿAffân ʿAbdulQâdir Al-Kowsî - وفقه الله.
[1] - Kasancewar Sa sama da HalittunSa
[2] - Istiwa, daidaituwar Allâh saman Al'arshinSa
[3] - Sauran ayoyin su ne Sûrah Yûnus (3), Sûrah Ar-Ra'ad (2), Sûrah Tâ-Hâ (5), Sûrah Al-Furqân (59), Sûrah As-Sajdah (4), Sûrah Al-Hadîd (4).