Ladubban Dalibin Ilimi - Shaykh Ibn Bãz


Matambayi yace:

Menene ladubban da ya kamata ɗalibin ilimi ya siffantu da su?

Amsa:

Ladubban Shariʾah [Qurʾãni da Sunnah], siffantuwa da tawadu'u, yaɗa sallama, amsa sallama, shiryarwa zuwa ga alheri, bayar da nasiha, umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, sadar da zumunci, karrama maƙoci, kamewa daga cutar da maƙoci, da ireren haka.

Waɗannan siffofi alamomi ne da suke nuni da alheri, kuma alamomi ne na cin nasara. Na'am.

Matambayi:

Allãh ya saka muku da alheri.

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial.

Daga
Previous
Previous

Yin Musharaka Da Kafirai Wajen Bikin Kirismeti (Christmas).