Yin Musharaka Da Kafirai Wajen Bikin Kirismeti (Christmas).


Tambaya :

Dan uwan mu yana cewa: yana lura da waɗansu musulmai suna mushakara tare da kristoci a maulidin [ʿĪsā b. Maryam], ko Krismeti (Christmas) kamar yadda suke kiran shi; yana fatan samun wani karin bayani game da wannan.

Al-ʿAllãmah ʿAbdul-ʿAziz b. ʿAbdillãh b. Bãz - Allāh ya jikan shi.

Bai halatta ga musulmi namiji ko mace suyi mushakara da kristoci, yahudawa, ko wasun su daga kafirai a bukukuwansu ba. Maimakon haka, wajibi ne ayi watsi da wannan. Wannan saboda [Annabi ﷺ yace]:

من تشبه بقوم فهو منهم

"Wanda ya kwaikwaiyi [wasu] mutane yana daga cikinsu."

Kuma Manzo (ﷺ) ya gargade mu daga kwaikwayonsu da kawata kanmu da halayensu. Saboda haka yana kan mumini namiji da mace yayi hattara da wannan, kuma kar da ya taimake su wajen shagalin wadannan bukukuwan da komai.

Wannan saboda bukukuwan sun sabawa Shari'ar Allãh kuma makiyan Allãh ne suka kafa su. Don haka baya halatta yin musharaka da su cikinsu ko hada kai da mutanensu ko taimakonsu da wani abu, ba ga (basu) shayi ba, kofi (gahawa), ko wani abu, kamar abubuwan cin abinci da girka abinci, da sauransu. Kuma, Allãh, Mai Daukaka yace:

وَتَعَاوَنُواْ عَلَى الْبرِّ وَالتَّقْوَى وَلاَ تَعَاوَنُواْ عَلَى الإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ

Kuyi taimakekeniya wajen Al-Birr da At-Taqwā (kyautatawa da tsoron Allãh); amma kar da kuyi taimakekeniya wajen zunubi da zalunci. [Al-Ma’idah : 2].

Don haka musharaka da kafirai a bukukuwan su wani nau'i ne na taimaka musu akan zunubi da zalunci. Don haka, wajibi ne akan kowane Musulmi namiji da mace suyi watsi da wannan kuma bai dacewa ga wanda yake da hankali ya zamanto ya rudu da mutane a ayyukansu. Wajibi ne nazari akan Shari'ar Musulunci da abunda ta kawo da yin riko ga umarnin Allãh da ManzonSa, kuma ba tare da yin duba zuwa ga al'amarin mutane ba. Domin mafi yawan halittu basu da damuwa da Sharee'an Allãh.

Kamar yadda Allah mafi Girma da Daukaka yace:

وَإِن تُطِعْ أَكْثَرَ مَن فِي الأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَن سَبِيلِ اللّهِ إِن يَتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلاَّ يَخْرُصُونَ

Kuma da zaka yi biyayya ma mafi yawan mutanen duniya, zasu batar da kai daga tafarkin Allãh. [Al-An'am : 116]

Shi, Mai Daukaka, yace:

وَمَا أَكْثَرُ النَّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُؤْمِنِينَ

Kuma dayawan mutane baza suyi imani ba koda kana kwadayin haka. [Yusuf : 103]

Haka bukukuwan waɗanda suka sabawa Sharee'ah, baya halatta amincewa da su, ko da mutane suna aikatawa. Domin mumini yana auna ayyukan sa da maganganun sa, da ayyukan mutane da maganganun mutane, ta hanyar Littafi da Sunnah; Littafin Allãh da Sunnar ManzonSa (ﷺ). Abunda yayi daidai da su ko daya daga cikinsu, ana karban sa, koda mutane sun yi watsi da shi. Abunda ya saba musu ko daya daga cikinsu, ana watsi da shi, koda mutane suna aikata shi. Allãh ya bamu nasara da shiriya gabaki daya.

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Fassarar turancin Raha ibn Donald Batts, Al-Manhajul ul-Haqq.

25/ Jumãda Al-Ulã/ 1444 هــ.

19/ December/ 2022.

Previous
Previous

Bayani Daga Kwamitin Manyan Malamai Game da Ikhwân-ul-Muslimîn (wato: ‘Yan Braza)

Next
Next

Ladubban Dalibin Ilimi - Shaykh Ibn Bãz