Manhaji (Hanyar) Na Ahlul-Sunnati wa-l-Jamaʾah

Salafiyyoon ana banbanta su ne da rikonsu zuwa ga asulan Manhaji waɗanda aka bayyana cikin littafin Allâh,sunnan Manzon Sa (ﷺ) da ayyukan Sahabbansa (Allâh ya kara musu yarda).

Domin haka,a fannin ʿAqîdah, magabata na ƙwarai suna bin hanya ta musamman wadda ta sãɓãwa waninta, na daga ash'ariyya, mu'tazilah da wasunsu waɗanda alamar da suka kebanta da ita (tambarin su) shi ne fifita hankali da Kalâm (theological rhetoric) bisa nassi na littafin Allâh da na sunnan ManzonSa (ﷺ) da sanannun kalaman Malaman Sunnah na wannan Ummah.

Haka kuma,a fannin ʿIbâdah (bautã), magabata na ƙwarai (Salafus Sâlih) suna bin hanya wadda ta ke adawa da hanyar sufaye (Sufis) da masu bautan kaburbura,waɗanda suke ƙirƙire- ƙirƙiren abubuwa cikin addini waɗanda Allâh bai saukar da hukuncinsu ba.

Haka kuma,a fannin Da'wah (kira zuwa ga Allâh) da al'amuran yau da kullun, Salafiyyûn suna banbanta daga ƙirƙirarrun Manhajin bogi na 'yan gwagwarmayan siyasa (political activists),waɗanda suke yaudara ta hanyar ɓuya bayan bin magabata na qwarai da sanannun Malamai wannan zamani,suna ingiza jama'ar gari,suna janye su daga kafaffun malamai sannan suna kiran (jama'ar gari) zuwa ga kawunansu.

Shaykh Sâlih al-Fawzân - [حفظه الله] - yace:

Dalilan rashin hadin kai suna da yawa. Daga cikin manya-manyan su sune: Na farko,adawa da manhajin (hanyar) magabata na ƙwarai, Sahabban Manzon Allâh (ﷺ) da waɗanda suka biyo su. Don haka magabatan ƙwarai sun kasance suna da Manhaj (hanyar) da sukayi riƙo dashi; Manhaji a ʿAqîdah, Manhaji a Daʾwah (kira zuwa ga Allâh), Manhaji a umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, Manhaji a yanda ake hukunci tsakanin mutane. Wannan shi ne Manhaj,a dukkan yanayi ya kasance akan Littafin Allâh da Sunnan Manzonmu (ﷺ).

[Wujoob ut-Tathabbut fil-Akhbâr p.18]

AMMAN CIRCLE EDITORIAL

1st Safar 1444 (هــ),

29 August 2022.

Previous
Previous

Bidi’o’i Suna da Haɗari