Falalar Azumtar Kwana Shida A Watan Shawwāl (Azumin Sitta Shawwāl)



Al-Imām Al-ʿAllāmah Shaykh ʿAbd Al-ʿAzīz b. Bāz - رحمه الله - Ya Ce:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allāh, aminci da salati ga Manzon Allāh da sahabbanshi da Duk wanda ya bi shiriyar sa, bayan haka.

Ya inganta daga Manzon Allāh - عليه الصلاة والسلام - cewa ya ce:

“Duk wanda ya azumci Ramadāna sannan ya bi shi da (azumtar) kwana shida daga watan shawwāl, zai kasance kamar azumin shekara.”

Muslim ya rawaito a sahihin shi. Kuma wannan yana nuni akan falalar sa (wato shi azumin sitta shawwāl) da cewar azumin kwana shida na Shawwāl tare da Ramaḍān tamkar yin azumin shekara dukkanta, kuma wannan falala ce mai girma, Ramaḍān sai ya zama daidai da watanni goma, shi kuma Sitta Shawwāl sai ya tsaya matsayin watanni biyu, shi aikin lada guda ana nunka shi sau goma, sai ya zama kamar ya azumci duka shekara.

Duk da cewar Allāh, saboda tausasawar sa, ya sanya Ramaḍān a matsayin kaffara ga zunuban da suke tsakanin Ramaḍān guda biyu, se kuma Sitta Shawwāl akwai ƙarin alheri a cikin su, da maslaha gagaruma, da fa’ida mai girma, a wajen aiwatar da umarnin Annabi - ‎ﷺ - da yin koyi da shiriyar shi - ‎ﷺ - da kuma kwaɗaitarwar da yayi, da dagewa wajen aikata abunda Allāh ya shar’anta na daga ibaada, kuma wannan babban alheri ne, sannan mumini yana ƙoƙarin sanin abunda Allāh ya shar’anta ne, kuma yana aiwatarwa yana mai neman lada daga Allāh, wannan yana da lada mai girma. Na’am.

Daga

Previous
Previous

Azumin Kwana Shida na Shawwāl Ga Wanda Yake Da Ramuwa Akan Shi - Al-‘Allāmah Ṣāliḥ al-Fawzān

Next
Next

Manufar Ita Ce Fahimta! - Shaykh Al-Islām Ibn Taymiyyah