Azumin Kwana Shida na Shawwāl Ga Wanda Yake Da Ramuwa Akan Shi - Al-‘Allāmah Ṣāliḥ al-Fawzān

Tambaya:

Menene ra’ayinku game da azumin kwana shida na Shawwāl ga wanda yake da ramuwa akan shi?

Amsa:

Abunda ya fi shi ne ya gaggauta wajen ramuwa, idan zai yiwu azumtar kwana shidan sai ya azumce ta, ma’ana muddin watan Shawwāl bai gushe ba an shar’anta azumin kwana shidan, sawa’an a farkon watan ne ko a tsakiyar shi ko a ƙarshen shi, don haka yayi gaggawa wajen ramuwa sannan ya yi azumin kwana shidan ko da a ƙarshen watan ne.


Daga

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial

Next
Next

Falalar Azumtar Kwana Shida A Watan Shawwāl (Azumin Sitta Shawwāl)