Menene Taqwá? - Shaykh ‘Ubayd Al-Jābirī
﷽
Al-‘Allāmah ‘Ubayd ‘ Al-Jābirī - رحمه الله - Ya Ce:
At-Taqwá shi ne kayi aiki wajen biyayya ga Allāh bisa haske daga Allāh kana mai sa rai a rahamar Allāh da kuma barin saɓon Allāh bisa ga haske daga Allāh kana mai tsoron azabar Allāh, kuma wannan yana da mataki guda uku:
1 - Aikata abun da aka umarta
2 - Barin abun da aka hana
3 - Kiyaye/ ƙauracewa shubuha (abubuwa masu kwokwanto).
Tanbīh Dhawī al-‘Uqūl as-Salīmah sh 66
Fassarar: AMMAN CIRCLE Editorials