(1) - Salafi Daʾwah Dangane da Sauran Jama'a.


Al-ʿAllãmah Al-Muhaddith Ash-Shaykh Muhammad b. Nãsir-ud-Dîn Al-Albãnî (رحمه الله):

Zan fadi kalami na gaskiya bayan wanda babu wani Muslmin da zai iya musawa bayan gaskiyar ta bayyana gareshi. Abu na farko, Da'awar Salafiyyah joni ce ga mene? "Salafî" joni ne zuwa ga "Salaf" (Magabaata na Ƙwarai), saboda haka sai mun san su wanene Salaf sannan menene ma'anar wannan jonin da kuma muhimmancin shi, ta fuskar ma'ana da kuma tasiri.

As-Salaf su ne mutanen ƙarni uku na farko waɗanda Manzon Allãh ‎(ﷺ) yayi shaidar ãdalar su a ingantaccen hadisin da yake (a darajar) mutawãtir, wanda Bukhãri ya rawaito da Muslim da wasu daga cikin Sahabbai cewar ya ce:

Mafifitan mutaane su ne ƙarni na, sannan waɗanda suka biyo bayansu sannan waɗanda suka biyo bayansu.

Waato ƙarni uku na farko. Saboda haka Salafiyûn suna jingina kansu ne ga Salaf, kuma idan mun san ma'anar 'Salaf' da 'Salafî' sai mu lura da abu biyu. Cewar wannan jonin ba zuwa ga mutum guda bane ba ko mutane, (ba kamar) yanda waɗansu jam'iyoyi da suke Duniyar Musulunci (Al-Ummah). Wannan ba joni ne zuwa ga mutum daya ko mutane goma ba, joni ne zuwa ga abunda ba zai kuskure ba, tunda ba zai taba yiwuwa Salaf suyi tarayya akan kuskure ba, sabanin mutanen lokutan dasuka biyo baya, tunda game da karnunnukan baya, babu nassi dayayi musu shaida (game da adalcin su). Hasali ma, a dunƙule an aibata su ne a ƙarshen Hadisin da ya gabaata: "Za a samu mutane da za su zo waɗanda zasu bayar da shaida kuma ba a nemi shaidarsu ba…" a kuma wani Hadisi aka samu: "wani yanki daga al’ummata bazasu shude da zama akan gaskiya ba…".

Domin haka wannan yabo ne garesu amma kuma aibuntawa ga sauran tunda yabon ya taƙaita ga wani yanki ƙarami (na mutane). A harshen Larabci "Tã'ifah" ana amfani da kalmar ne wajen magana kan mutum daya ko sama da haka. Saboda haka idan muka fahimci ma'anar "Salafîs" (Salafiyûn) da kuma cewar sun jingina kawunansu zuwa ga Salaf ne - kuma cewar idan Musulmi ya yi riko da abunda Salaf suke kai - yanzu mun iso mas'alah ta biyu:

1) Cewar bayan an fahimci wannan, babu makawa saidai kowane Musulmi ya zama Salafî, tunda mun fahimci cewar a jingina kai zuwa ga salaf mutum ya jingina kanshi zuwa ga abunda ba zai kuskure ba. An dauki wannan ne daga Hadisin; "al'umma ta baza ta taru akan kuskure ba."

2) Kuma baya ya inganta yin amfani da ma'anar wannan a (wajen siffanta) mutanen baya baya; waɗanda suke mutanen wannan lokacin. Daɗin-daɗawa ga wannan shi ne Hadisan da suke yin magana game da abunda ya faru ga mutaanen dasuka gabaata- yahudawa da Nasara (Kiristoci) - da kuma abunda zai auku ga Musulmai, game da rarrabuwa zuwa ƙungiyoyi, fadinsa:

Yahudawa sun rarrabu zuwa kashi saba’in da daya, kiristoci kuma kashi saba’in da biyu, al’umma ta zata kasu zuwa kashi saba’in da uku. Dukkaninsu suna wuta faace guda daya. Sahabbai suka ce: "Su wanene su ya Manzon Allãh ‎()?" Ya amsa: "Su ne al-Jamã'ah."

Wannan yayi nuni ga waɗanda ake nufi a Hadisin da ya gabaata "Al'ummata baza tayi tarayya akan kuskure ba." Tunda su ne kubutacciyar kungiya, tare da waɗanda suke da irin ra'ayinsu kuma suka bi su. Su Salafus-Salihîn su ne waɗanda Allãh ya yi mana gargadin ƙalubalanta ko bin tafarkin da ba nasu ba, fadinShi:

وَمَن يُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ ٱلْهُدَىٰ وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ ٱلْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصْلِهِۦ جَهَنَّمَ ۖ وَسَآءَتْ مَصِيرًا

Duk wanda ya saɓawa Manzo bayan shiriya ta zo mishi kuma ya bi hanyar da ba ta muminai ba, zamu bar shi a tafarkin da ya zabar wa kanshi kuma mu shigar da shi wuta- tir ga wannan makoma!

- Sûrah An-Nisã' : 115



Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Salafi Publications (Birmingham, UK).

Daga: http://www.salafipublications.com/sps/sp.cfm?subsecID=SLF02&articleID=SLF020002&articlePages=2

Previous
Previous

Kiran Kanka Salafi

Next
Next

Tafarkin Sahabbai - Tafarki Guda Na Samun Tsirã.