Tafarkin Sahabbai - Tafarki Guda Na Samun Tsirã.


Manzon Allãh [Tsira da amincin Allãh su tabbata agareshi] yace:

Haƙiƙa wanda yayi tsawon rai acikin ku zai ga rarrabuwa mai yawa, kuma kashedinku daga kirkirarrun al’amura [a addini] domin bata ne. saboda haka Duk wanda  ya iski (wannan lokaci) a cikinku gareshi ne yin riko da sunnah ta da sunnar shiryayyun kalifofi, ya ciza ta da turamen sa (wato ya yi riko da ita da ƙarfi). [1]

Imãm Ibn Rajab [Allãh yayi mishi rahama] yace:

Cikin wannan Hadisin (ne) umarnin cewar idan rarrabuwa da kasuwa ta auku, [mutum ya] riko Sunnar Manzo ‎(ﷺ) da Sunnar Kalifofi [Allãh ya yarda da su] bayansa. Sunnah ita ce tafarkin da ya daace a lizimta kuma kunshi abunda shiryayyun Kalifofi suke kai na daga Akida, ayyuka da kuma zantuttuka. Wannan shi ne cikakkiyar Sunnah. [2]

Abdullãh Ibn Mas'ûd (رضي الله عنه) yace:

Duk wanda yake son lizimtar wani tafarki, toh ya lizimci tafarkin waɗanda suka gabaata domin na rãye basu aminta daga fitina ba, kuma su (waato waɗanda suka gabaata) sune Sahabban Manzon Allãh. Sune mafifitan wannan Al'ummar, sune Ma'abota mafi kyawun zukaata, mafi kammaluwa a ilimi kuma mafiya rashin rikici. Allãh ya zaɓe su da rakiyar (waato saahibantar) Annabin-Shi ‎(ﷺ), da kuma tsaida Addini. Saboda haka mu san muƙãminsu (da darajar su), mu bi sãwunsu kuma muyi iya ƙoƙarinmu wajen yin riko da halayensu domin tabbas sun bi haƙiƙanin shiriya. [3]

Imãm Ibn Rajab Al-Hanbali (Allãh yayi mishi rahama ya ce):

Ba za a samu a cikin kalaaman waɗanda suka zo bayan Salaf kowace gaskiya ba faace se an saame ta a cikin kalaamansu (Salaf) a takaitacan lafazi dakuma takaitacciyar siga.

Ba (kuma) za a samu cikin kalaaman waɗanda suka zo bayansu wani ɓata/ƙarya ba faace an samu cikin kalaaman su (Magabaata na Kwarai) abunda zai bayyana ƙaryar shi, ga wanda ya fahimta kuma yayi nazari [waato wanda ya fahimci kalaaman Salaf]. Akwai kyawawan ma'anoni da za a samu cikin kalaamansu da daidaitattun nazarinsu, wanda ba'a shiryar da waɗanda suka zo bayansu ba zuwa gareshi kuma basu san shi ba.

Wanda bai dauki ilimi daga kalaamansu ba zai rasa dukkanin wannan alherin, tare da yawan (al’amuran) bata da zai afka ciki sanadiyar bibiyan waɗanda suka zo bayansu [wato sanadiyar yin waatsi da Salaf (Magabaata)) da kuma bibiyar waɗanda suka zo bayansu]. [4]

Bayanin Kula


[1] - Ruwaito daga Ahmad: 4/126; Abu Dãwud 4607; Tirmidhee 2676; Ibn Mãjah 43.
[2] - Jaami-ul Uloom Wal-Hikam: pg 249.
[3] - Jaami Bayaan Al-Ilm Wa Fadlihi 2/947.

[4] -  Fadl Ilm As-Salaf Alaa Ilm Al-Khalaf' shaafi 61. da sauyin kalma kadan.

* Salaf su ne Magabaata na Kwarai, su ne karni ukun nan na Musulunci da Manzon Allãh (ﷺ) ya yabesu, waato Sahabbai, Tabi'ai da Atba'ut-Tabi'een.

Domin karin bayaani akan Salaf, Danna nan.  

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Salafi Centre of Manchester, UK.

25 Rabiʾ Ath-Thãni 1444 (هــ).

20 Nov 2022.

Previous
Previous

(1) - Salafi Daʾwah Dangane da Sauran Jama'a.

Next
Next

Salaf Sune Ma'abota Sunnah