Menene Salafiyya? Kuma Ga Me Take Kira Zuwa (1-10)

1. Muna kira, da farko, zuwa ga bautar Allāh shi kadai ba tare da yin shirka da Shi ba. Wannan shi ne wurin kira na farko na Annabawa (عـلـيـهـم الســـلام) kamar yadda Allāh ya fadi:

“Mun tura manzo zuwa ko wace al-ummah yana kiran: “[ku] Bautawa Allah shi kadai kuma ku gujewa bautar iyayen-gijin karya.” (Sūrah An-Naḥl : 36)

Domin haka, wannan kiran zuwa bautawa Allāh shi kaɗai dole sai an hada ta da kore bautar komai koma bayanShi.

2. Mun amince cewa addini yana kira zuwa ga muhimmanin abubuwa, don haka, muna farawa da mafi muhimmancin al’amari, sannan wanda ya biyo bayanshi a mahimmanci, bisa ga nassin Qur’āni da Sunnah. Manzon Allāh (ﷺ)  ya umurce Muā’dh b. Jabal (رضي الله عنه):

“Ka kira su da farko zuwa ga bautawa Allāh shi kaɗai, idan sun tabbatar da hakan, sannan ka gaya musu Allāh ya wajabta akan su salloli biyar a dare da rana. Idan sun tabbatar da hakan, sannan ka gaya musu Allāh ya wajabta Zakah akan su…” (Ṣaḥīḥ  Muslim #19)

3. Mun rike [cewa] Sunnah Wahayi (Waḥy) ne kamar yadda Qur’āni wahayi ne. Allāh, Mafi Girma, yace:

“Shi (Annabi) bai magana daga raayinsa, maimakon haka bai kasance [hakan ba] faace wahayi ce da aka tura mishi.” (Sūrah An-Najm : 3 - 4)

4. Mun yi imani da Sunnah ita ce duk wani abu da aka saukarwa Annabi (ﷺ) bayan Qur’āni. Annabi (ﷺ) yace:

“Lallai an bani Qur’ani da wani abu makamancin shi tare da shi.” (Sunan Abī Dāwūd 4604)

5. Mun yi imani da Sunnah ita ce duk wani abu da Annabi (ﷺ) ya fadi, ko yayi, da duk abunda aka yi a gaban shi wanda bai yi hani akai ba. Kuma Sunnah ta kunshi Kamannin shi da kuma halayenshi.

6. Mun riki cewar mafifitan mutune bayan annabawa da manzanni (عـلـيـهـم الســـلام) sune Sahabban Annabi Muḥammad (ﷺ) dan cewar sa [shi ﷺ]:

“Mafifitan mutane sune qarni na, sannan waɗanda suka zo bayan su, sannan waɗanda suka zo bayan su.” (Ṣaḥīḥ Al-Bukhārī 6429)

7. Mun riki cewar mafi nagartar waɗannan Sahabban shi ne Abū-Bakr As-Ṣiddīq, sannan ʿUmar b. Al-Khaṭṭāb, sannan ʿUthmān b. ʿAffān, ʿAlī b. Abī Ṭālib (رضــي الله عنهــم), sannan ragowar Sahabbai guda goma da akayiwa alkwarin Al-Jannah. Sannan, waɗanda suka yi yaki a Badr, sannan waɗanda suka yi mubaya’a a Al-Ḥudaybiyah a karkashin bishiyar Ar-Riḍwān, sannan ragowar Muhājirūn, sannan Anṣar, sannan waɗanda suka karbi Musulunci kafin Fatḥ-ul-Makkah, sannan waɗanda suka karba bayan Fatḥ-ul-Makkah.

8. Mun barranta kanmu daga [Rāfiḍah] Shi’ah kuma muna gargadi akan su da bidio’in su waɗanda basu da adadi kamar ƙiyayyarsu, [da] zagi, [da] tsinewa maatan Manzon-Allāh da Sahabban shi (ﷺ). Manzon-Allāh (ﷺ) yace:

“Kada ku zagi sahabbai na, na rantse da Wanda raina ke Hanun sa, in daya daga cikin ku zai bayar da kwatankwacin dutsen uhudu a zinari, ba zai kai kwatankwacin cikin tafin hannun daya daga cikin su ba, kai ko rabin [cikin tafinsu].” (Ṣaḥīḥ  Al-Bukhārī 3673)

Kuma shi (ﷺ) yace:

“Tsinuwar Allāh na kan wanda ya tsine wa Sahabbai na.”

(Al-Mu'jam Al-Awsaṭ - 7015 - na Imām At-Tirmidhī | Al-Muḥaddith Shaykh Al-Albānī yace Ḥassan [Kyau] a Ṣaḥīḥ  Al-Jāmiʿ - 5111)

9. Mun yi imani cewa gyaran al ummah yana cikin riko da Littafin Allah da Ingantacciyar Sunnar Manzon-Allāh (ﷺ) akan fahimtar Sahabbai. Annabi (ﷺ) yace:

“Na bari acikinku [wani abu] wanda idan kukayi riko da shi, baza ku taba bata ba: Littafin Allāh (Al-Qurʾān) da Sunnah na.” (Ṣaḥīḥ  Muslim 1218)

Ya kuma ce:

“Ku yi riko da Sunnah na da Sunnan Kalifofi shiryaryu bayan na.” (Daga Abū Dāwūd, Ḥadīth 28 a Hadisi Arba'in na Al-Ḥāfidh An-Nawawī)

10. Mun yi imani da samun hadin kan Musulmai da kuje wa rabuwan [Muslmai] Aṣl (daya daga cikin muhimman ka'idoji) ne [da] Allāh da Manzon Sa (ﷺ) suka umurce mu da. Allāh, Mafi Girma, Ya fadi:

وَٱعۡتَصِمُواْ بِحَبۡلِ ٱللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا۟ۚ

“Ku yi riko dukkanin ku tare ga Igiyar Allāh, kuma kar ku rabu.” (Sūrah Āl-ʿImrān:103)

Kuma Shi Yace:

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱخۡتَلَفُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُۚ

“Kar ku zamo irin waɗanda suka rabu kuma suka yi tsabani bayan hujjoji bayananne ya zo musu.” (Sūrah Āl-ʿImrān:105)


Sh. 4-7 Menene Salafiyya? Kuma Ga Me Take Kira Zuwa na Abû Khadeejah ʿAbdulWâhid Alam (‏حفظه الله) | Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial | An fassara da izinin Shaykh Abû Khadeejah ʿAbdul-Wâhid Alam (‏حفظه الله)
Next
Next

Menene Salafiyya? Kuma Ga Me Take Kira Zuwa (Muqadimah)