Menene Salafiyya? Kuma Ga Me Take Kira Zuwa (Muqadimah)
﷽
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allâh, Ubangijin dukkanin halittu. Allâh ya kara daukaka ambaton Annabi a cikin mafi daukakar tawaga ta mala'iku, tsira da aminci su tabbata agare shi da iyalen shi, da sahabban shi da duk waɗanda suka bishi daidai (a kyautatawa) har zuwa ranar sakamako.
Bayanin Waɗansu Kalmomi (Dake Da Alaka da Salafiyyah)
✒ Musulunci shi ne addinin dukkanin annabawa, daga Adam zuwa Muḥammad (ﷺ). Musulmi shi ne duk wanda ya karbi wannan addinin kuma yayi aiki da shi. Musulmai basa bautawa kowa faace abin bautawa na gaskiya (Larabci, Al-Ilah), kuma shi ne Allâh. Musulmai sun kauracewa duk wani nau'in Shirka kuma suna bin koyarwar Manzo na karshe (ﷺ) da aka tura ga mutane. Wannan shi ne tubalin Salafiyyah.
✒ Sunnah itace tafarkin Annabi (ﷺ) da Sahabban sa. Duk wanda ya bi wannan tafarkin daidai (da kyautatawa) ana kiranshi da sunan 'Sunnî' kuma yana daga Ahl-ul-Sunnah wal Jamâʾah. Waɗansu lokutan kalmar Sunnī ana amfani da ita gamagari (wa kowa) domin nuni ga duk wanda baya daga cikin kungiyar Shi'a. Amma duk da haka rashin zama Shi'a baya wadaatarwa wajen ceton mutum daga fadawa cikin bata.
✒ As-Salaf As-Sâlih (Magabata na Kwarai) sune Sahabban Muḥammad (ﷺ) da karni guda uku da suka zo bayan su. Kuma ana kiransu da Ahl-us-Sunnah wal Jamâʾah, Salaf, Ashâb-ul-Hadîth da Ahlul-Hadîth. Duk wanda ya yarda da su kuma ya bi tafarkinsu daidai a Aqeeda (ʿAqîdah), Manhajin (Manhaj), da addini [lallai] yana kan haƙiƙanin shiriya.
✒ Salafiyyah itace asalin hanya a bin Musulunci da Sunnah. Salafi shi ne wanda yake bin hanyar Salaf As-Sâlih [bisa] daidai [ba tare da] canja [komai ba, ta hanyan kari ko ragi].
✒ Kalmar Salafi, Sunni, Ahl-us-Sunnah wal Jamâʾah, Ashâb-ul-Hadīth da Ahlul-Hadîth ana amfani da su a madadin juna. Dukkanin sunayen suna nuni zuwa (jinsin) mutane daya ne, waɗanda duk suke bin hanya iri daya. Amma duk da haka, ba duka masu yin amfani da waɗannan laqabin ne suke bin abinda suke wakilta a gaskiya ba. Hasali ma, mafi yawancin mutanen da suke jingina kansu zuwa waɗannan laqabin sunada Aqeeda da Manhajin dake kalubalantar hanyar Salaf As-Sâlih. Iya bambance mai jingina-kai kawai da wanda yake riƙa da bi da gaskiya shi ne asalin manufar rubuta wannan makalar.
Zama Salafi shine riko da bin Aqeeda, Manhajin da hanyar rayuwar Salaf As-Sâlih (Magabata na Kwarai). Qarnin Annabin mu (ﷺ) da Sahabban sa sune farko-farkon Salaf. Sai bayan su qarni guda uku na Mu'uminai suka zo waɗanda suka rike Sunnah (hanyar) Annabi (ﷺ) da Sahabban sa.
Mutumin da ya fahimci wannan hanyar daidai, ya bita daidai, ba tare da gabatar da ko wane [irin] sabon abu cikin ta ba kuma bai karkace daga hanyan ba shi ne Salafî. Zama Salafî ba wai kawai [mutum] yayi tunanin kawai ai yana kan hanyar asalin Salaf ba, amma Salafiyyah ita ce koyon (neman sanin) addinin sahabbai da kuma bin shi - sune waɗanda suke [da] mafi ingancin fahimta game da ma’anoni da manufar maganganu da ayyukan Annabi (ﷺ). Don haka, inda wani ya tambaye ka: "Menene kiran mu (Daʾwah) da Manhajin (Manhaj) Salafis wajen koyo, ɗabbaƙãwa, da koyar da Addini?"
Zamu iya amsawa ta [hanyar] cewa : Ga Da'war mu anyi bayanin ta a maki 89 masu zuwa.
Sh. 3-4 Menene Salafiyya? Kuma Ga Me Take Kira Zuwa na Abû Khadeejah ʿAbdulWâhid Alam (حفظه الله) | Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial.