Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. Bâz Ya Amsa Tambaya; Menene Salafiyyah?
﷽
Tambaya:
Menene As-Salafiyyah kuma menene ra'ayinka gameda hakan?
Jawabi:
Dukkan godiya ta tabbata ga Allâh shi kadai, aminci da rahama su tabbata ga Ma'aikinsa , da Ahalinsa da Sahabbansa.
Zuwa ga cigaba:
"As-salafiyyah" yana ta'allaqa ne da 'salaf', kuma "salaf" sune sahabban Manzon Allâh (ﷺ), da kuma shugabannin musulunci shiryayyu daga qarni ukun farko, wadanda Manzon Allâh (ﷺ) yayiwa kyakyawar shaida cikin fadinsa:
" Mafi alkhairan mutane sune karnina, sanan mabiyansu, sannan mabiyansu, wasu mutane zasu zo wadanda shaidarsu zata fi alkawarinsu da kuma alkawarinsu zatafi shaidar su."
[An rubuto daga Imâm Ahmad ibn Hanbal cikin Musnad, Al-Bukhârî, da Muslim] - (1)
Kuma "salafiyoon" shine jimlar " salaf", Wanda ya ta'allaqa da salaf, kuma an yi maganar ma'anar a baya- sune wadanda suke bin Manhajin Salaf ta hanyar amfani da littafin Allâh (Al-Qurʾân) dakuma sunnar Manzon Allâh (ﷺ), dakuma gayyato mutane gareta, dakuma aiki dasu, sabida haka suka zama Ahlus-Sunnah wa-l-Jamaʾah.
(1) Imâm Ahmad:(4/426). Al-Bukhârî: (2651). Muslim:(2535).
Shaykh ʿAbdul -ʿAzîz Bin Bâz (رحمه الله عليه)
Fataawa Al-Lajnah Ad-Dâ'imah: (2/165-166). Fatwa No. (1361).
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial.