Su Wanene Salaf?

Tambaya: Ina Jin maganganu dayawa game da Salaf, su wanene Salaf Ya Shaykh [Ibn 'Uthaymin - Allah yayi mishi rahama]

Amsa: Ma'anar [kalmar] Salaf ita ce Al-Mutaqaddimoon (Magabaata) don haka duk mutumin da ya riga wani ya zama Salaf a gare shi. Amma idan akayi amfani da wanna kalma ba tare da iyakancewa ba (wato mutlaqan) toh kawai tana nufin al'ummomi uku na farko da aka yaba- daga Sahabbai da Tabi'ai (wadanda suka biyo bayan su) da wadanda suka biyo bayan su (wato Atba' at-Taabi'een).

Lallai su Salaf as-Salih (Magabaata Na Kwarai) duk wanda ya zo bayansu, Kuma ya bi Manhajinsu (hanya da tafarkinsu) to, zamanto kamar su a hanyar Salaf (Magabaata) ko da kam yana iya kasancewa ya zo bayansu a fuskar zamani domin as-Salafiyyah siffa ce da ta shafi Minhaj (hanya da tafarki) da Salaf As-Salih (Magabaata Na Kwarai) suka bi, kamar yadda Annabi (ﷺ):

"Hakika al'ummata za ta kasu kashi saba'in da uku dukkansu suna a cikin wuta face daya kuma ita ce al-Jamâ'ah (Uwar Jikin Musulmai)."

Da kuma a wani lafazin: ".. duk wanda ya kasance a kan abin da nake a kai da Sahabbaina."

Domin haka Salafiyyah anan ta kebanta a ma'ana, don haka duk wanda yake kan Minhaaj (tafarkin) Sahabbai da Taabi'ai da wadanda suka bi su da kyautatawa to shi Salafi ne ko da kuwa yana cikin wannan zamanin namu na karni na sha hudu muke ciki bayan hijira (Hijirar Annabi (ﷺ) daga Makkah zuwa Madînah).

Shaykh Muhammad b. Salih al-'Uthaymin Fatâwâ Nûr 'Alâ al-Darb (1/35).
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Fassaran Turancin Aboo 'Abdillaah Bilaal Hussain al Kashmiree.
Previous
Previous

Salaf Sune Ma'abota Sunnah

Next
Next

Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. Bâz Ya Amsa Tambaya; Menene Salafiyyah?