Ɓoyayyiyar Shirka


Wannan nau'i na uku an yi ishara zuwa gareshi a fadin Annabi ‎(ﷺ):

"Shin ba zan sanar da ku abunda na ke ji muku tsoro fiye da dajjal ba?" Sahabbansa suka ce: "Ae ya manzon Allãh." Shi ‎(ﷺ) yace: "Ɓoyayyiyar shirka: mutum ya tsaya sallah sai ya ƙawata sallarshi domin ya ga wani mutum na kallonshi."

Imãm Ahmad ya rawaito a Musnad dinshi daga Abû Sa'id Al-Khudri, Allãh ya kara yarda da shi.

Ana iya kuma kasa Shirka gida biyu kaɗai, Babba da ƙarama.

Amma Ɓoyayyiyar Shirka, ta game duka biyu domin wani lokacin tana aukuwa a Shirka Babba kamar Shirkar Munafukai - suna ɓoye akidunsu na ƙarya, suna bayyana Musulunci. Wannan ya kasance ne saboda suna ƙokarin nunawa (da birge) wasu kuma suna ji wa kansu tsoro.

Ɓoyayyiyar Shirka tana iya aukuwa kuma a Shirka karama misali riya (yin ayyuka domin birge wasu ba don Allãh ba). Misalin inda wannan yake faruwa shi ne abunda ya zo a hadisan nan biyu na baya, daya daga Muhammad bin Lubayd Al-Ansari, Allãh ya kara mishi yarda, da dayan daga Abu Sa'id, Allãh ya yarda da shi. Kuma nasara daga Allãh ta ke.

Bayanin Muhimman Darussa (ga kowane Musulmi) na Shaykh 'Abdul-'Azîz b. Bãz (رحمه الله).

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Darussalam Publishers, UK.

Next
Next

Ire-Iren Shirka: Shirka Ƙarama