Ire-Iren Shirka: Shirka Ƙarama


Ita ce wadda aka kira Shirka a Qur'ãni ko Sunnah, amma wadda ba ta cikin jinsin Shirka Babba. Misali, aikata wasu ayyuka domin Riya (don a gani a yaba ba don Allãh shi kaɗai ba), rantsuwa da wannin Allãh, cewa "abunda Allãh ya so kuma abunda abunda wane-da-wane ya so" da sauransu. Annabi (‎ﷺ) yace:

“Abunda nafi ji muku tsoro shi ne shirka ƙarama. Yayin da aka tambaye shi mecece ita shi ‎(ﷺ) ya ce: Riyã (yin ibaada domin wasu su yaba ba don Allãh shi kadai ba)”.

Imãm Ahmad ya rawaito, da Ɗabarãnî da bayhaqi daga Mahmud bin Lubayd Al-Ansari, Allãh ya yarda da shi, da Isnadi Hasan. Haka zalika an rawaito daga at-Tabarani da isnadi mai kyau, daga Mahmud bin Lubayd daga Rafi' bin Khadij daga Annabi (صلى الله عليه وسلم).

Manzon Allãh ‎ﷺ yace:

“Duk wanda yayi rantsuwa da wanin Allãh ya aikata Shirka”.

Imam Ahmad ya rawaito da ingantaccen isnadi daga ‘Umar bin Al-Khattab, Allãh ya kara mishi yarda.

Abu Dawud da At-Tirmithi sun rawaito da Isnadi Ingantacce daga rewayar Ibn ʿUmar, Allãh ya kara yarda da shi, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewar yace:

“Duk wanda yayi rantsuwa da wanin Allāh ya kafirta, ko kuma ya aikata Shirka”. 

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:

Kar kace: "Abunda Allāh ya so da kuma abunda wane-da-wane ya so." Kace: "Abunda Allāh ya so sannan abunda wane-da-wane ya so."

Abu Dawud ya rawaito wannan ne da isnadi ingantacce daga rewarayar Hudhayfa bin al-Yaman Allãh ya kara mishi yarda.

Duk da cewar wannan nau’in ba ya nufin cewa mutum ya fita daga addini, ko zai dawwama a wuta, yana nuni ga gazawar mutum wajen cimma darajar nan ta cikar Tauhidin da ta ke wajibi.

Bayanin Muhimman Darussa (ga kowane Musulmi) na Shaykh 'Abdul-'Azîz b. Bãz (رحمه الله).

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Darussalam Publishers, UK.

Previous
Previous

Ɓoyayyiyar Shirka

Next
Next

Ire-Iren Shirka: Shirka Babba