Daga Hadarurrukan Shirka

Dukkanin yabo ya tabbata ga Allâh, muna yabon shi, kuma muna neman taimakon Shi da gaafararshi. Muna neman tsarin Allâh daga sharrin kawunanmu daga kuma sharrin ayyukanmu. Dukkan wanda Allâh ya shiryar babu mai batar da shi kuma dukkan wanda Allâh ya baatar babu mai shiryar dashi. Na shaida cewa babu abun bautawa da cancanta sai Allâh, shi kadai ba tare da kishiya ko abokin tarayya, da kuma cewar Muhammad (ﷺ) bawan Sa ne kuma Manzon Sa. bayan haka:

Shirka itace bautawa wanin Shi (waato wanin Allâh) tare da shi. Shirka ba kawai bautan gunki bane kamar yanda aka koyarda da yawanmu, hattâ ar-Riyâ (yin ayyuka domin wanin Allâh) ko son wasu su ji ayyukanka na alheri nau'i ne na Shirka.

Bari in bamu misaali, dayanmu na tsaye da dare domin Qiyām-ul-Layl (Sallar Dare), sai wani ya shigo dakin, nan taake sai ka faara kãyata karatunka, ka kaara gyara tsayuwarka, la'alla ma ka soma kuka- amma duk ka yi hakan ne domin kawai wani ya shigo daakin. Sannan yi tunanin misali da rana sai mutumin ya dinga sosa bayanshi idan aka tambayeshi meya faru sai yace; "babu komai, na tsaya ne kusan tsawon awa biyu a sallar dare jiya"- Amma kawai ya fadi wannan ne domin mutane su san cewa yayi Qiyâm-ul-Layl; wadannan misalai ne na Shirka.

Sannan Shirka ita ce mafi tsanani, mafi hadari kuma mafi halakarwan dukkan zunubai. Girman ta a matsayin zunubi ya fi (mutum) yayi tarayya da mahaifiyarshi.

Sannan ka sani, Allâh ya sanyaka daga cikin ma'abota Tauhîdî, cewar Shirka ita ce mafi girman zalunci. ita ce bayarda haqqin Allâh zuwa ga waninsa, kamar yanda Luqmân ya sanar da dansa a al-Qurʾâni.

Sannan (tuna) lokacin da Luqmân (عليه سلام) ya ce da danshi yayin dayake mishi nasiha:

وَإِذْ قَالَ لُقْمَـٰنُ لِٱبْنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَـٰبُنَىَّ لَا تُشْرِكْ بِٱللَّهِ ۖ إِنَّ ٱلشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ

"Ya da na! kar ka hada wasu a wajen bauta da Allâh, lallai, hada wasu a bauta da Allâh zalunci ne babba.

Sûrah Luqman 31:13

Cikin Al-Qurʾâni, Allâh (عز وجل) yace dangane da wadanda suka mutu akan Shirka, wannan babban zaluncin;

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِۦ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفْتَرَىٰٓ إِثْمًا عَظِيمًا

Lallai, Allâh baya yaafe sanya abokan tarayya da shi wajen bauta, amma yana yaafe koma baayan haka ga wanda ya so, kuma duk wanda ya sanya kishiya da Allâh wajen bauta ya kirkiri babban zunubi.

Sûrah An-Nisâʾ: 48

Domin haka, mutum zai iya aikata Shirka ta hanyar daukan wanin Sa (Allâh سبحانه وتعالى) a matsayin abun bauta - Wannan ita ce Shirka a haqqin Allâh na bautâ. Mutum kuma zai iya aikata Shirka a Rububiyyah (Ubangijintaka) ta Allâh ta hanyar jingina Ubagijintaka zuwa ga wanin Sa- Misaali; yin da’awar cewar ‘Mother Nature’ ,waato ita ce ta saukar da ruwa ba Allâh ba.

Zai iya yiwuwa kuma Shirka ta kasance a Asmâ was-Siffât (Sunaye da Siffofi) na Allâh, ta hanyar jingina daukâkan sunayenshi da Siffofin Shi zuwa ga wanin Shi.

Waɗannan suna daga cikin hadarurruka na Shirka:


1 ) Wanda ya aikata Shirka an haramta mishi Al-Jannah.

Allâh (جلّ جلال) ya gaya mana a suratul Mâʾidah Âyah ta 72:

إِنَّهُۥ مَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِ ٱلْجَنَّةَ وَمَأْوَىٰهُ ٱلنَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ

….Lallai, duk wanda ya sanya wa Allāh kishiya wajen bauta Allâh ya haramta mishi Al-Jannah kuma makomarsa wutâ. Kuma ga az-Zalumai (masu Shirka da masu aikata laifi) babu mataimakâ.

2 ) Wanda ya aikata babbar Shirka, dukkanin ayyukansa kyâwâwâ zasu zamo a banza.

وَلَقَدْ أُوحِىَ إِلَيْكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ

Lallai an yi maka wahayi (Ya Muhammad ‎ﷺ ), kamar yanda akayiwa waɗannan (Manzannin Allâh) gabâninka: “Idan ka hada wasu wajen bautar Allâh, (toh) tabbas (duka) ayyukanka zasu zamo marasa amfani kuma zaka zamo daga cikin hasaararru”

Az-Zumar 39:65

A wata ayar, Allâh (ﷻ) ya kuma gaya mana abunda zai auku ga ayyukan waɗanda suka sanya abokan tarayya da Shi, ko suka bauta wa waninsa tare da Shi:

وَقَدِمْنَآ إِلَىٰ مَا عَمِلُوا۟ مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَـٰهُ هَبَآءً مَّنثُورًا

Kuma zamu gabaata zuwa ga abunda su (Kaafirai, mushirikai, masu zunubi) sukayi, kuma mu sanyasu kamar ƙûrâ wâtsatsiya.

Furqân 25:23

3 ) Duk wanda yayi shirka bashida hasken Allâh a duniyar nan da Lâhira.

Allâh yana fada mana a Sûrah az-Zumar, Âyah 22:

أَفَمَن شَرَحَ ٱللَّهُ صَدْرَهُۥ لِلْإِسْلَـٰمِ فَهُوَ عَلَىٰ نُورٍ مِّن رَّبِّهِۦ ۚ فَوَيْلٌ لِّلْقَـٰسِيَةِ قُلُوبُهُم مِّن ذِكْرِ ٱللَّهِ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ

Shin shi wanda muka bûda masa ƙirjinsa ga Musulunci ta yanda yakasance cikin haske daga Ubangijinsa (daidai yake da wanda yake ba Musulmi ba)? Saboda haka boni ga waɗanda zukatansu sukayi tauri kan ambaton Allâh! Suna cikin kuskure bayyananne!

4 ) Wanda ya aikata Shirka ba zai samu ceton Manzon Allâh ba ‎(ﷺ) Ranar Al-Qiyâmah.

Abû Hurayrah (رضي الله عنه) ya rawaito;

Nace; “Ya Manzon Allâh ‎ﷺ! Wanene zai kasance mafi dacewar mutane wanda zai samu cetonka Ranar al-Qiyâmah?” Manzon Allâh ‎(ﷺ) ya ce: “Ya Abû Hurayrah! Nayi tsammanin babu wanda zai tambayeni akanshi kaafinka domin nasan kwadayinka na (koyon) hadisai. Mafi daacewar mutane da zai samu cetona shi ne wanda ya ce da gaskiya daga zuciyarsa “Babu abubuwan da ya cancanta a bautawa sai Allâh”

Sahîh al-Bukhârî, 99

5 ) Wanda yake kan shirka zai rayu rayuwa mai kunci da damuwa. Kuma zai fuskanci azaba a Lâhira.

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَأُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا شَدِيدًا فِى ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Amma waɗanda suka kâfirce, zan azabtar da su da azaba me tsanani a duniyarnan kuma a lâhira basuda masu taimakamusu.

Sûrah Âl-ʿImrân:56

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ ذُو ٱنتِقَامٍ

Haqiqa waɗanda suka kâfircewa ayoyin Allāh, garesu ne azaba mai tsanani, kuma Allâh shi ne Maɗaukaki, Mai qudura wajen Ramuwa.

Sûrah Âl-ʿImrân:4

Waɗannan kadanne daga cikin hadarurrukan shirka. Wajibi ne akanmu musulmai mu koyi waɗannan al’amura da suke kaiwa zuwaga shirka, ta yanda zamu ƙaurace musu. Dole mu san sharri domin mu guje masa.

Ina roƙon Allâh سبحانه ya kaare mu daga shirka ya kuma nisantar damu daga ita da mutanenta.

AMMAN CIRCLE EDITORIAL (وفقهم الله),

1 August 2022.

Previous
Previous

Ire-Iren Shirka: Shirka Babba