Ire-Iren Shirka: Shirka Babba
﷽
Nau'in Shirka guda uku ne:
1). Shirka Babba
2). Shirka ƙarama
3). Ɓoyayyiyar Shirka
Shirka Babba
Wanda ya mutu akan ta, babbar shirka tana janyo rushewar ayyuka da kuma dawwamã a gidan wuta. Allãh Mafi girma Yace:
وَلَوْ أَشْرَكُوا۟ لَحَبِطَ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
Amma da sun haɗã a bauta wasu tare da Allãh, da dukkan abunda suka kasance suna aikatawa bazai amfane su ba.
- Sûrah Al-An'aam : 88.
Kuma Allâh Yace:
مَا كَانَ لِلْمُشْرِكِينَ أَن يَعْمُرُوا۟ مَسَـٰجِدَ ٱللَّهِ شَـٰهِدِينَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِم بِٱلْكُفْرِ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَـٰلُهُمْ وَفِى ٱلنَّارِ هُمْ خَـٰلِدُونَ
Bai kasance ga mushirkai su yi hidimar masallatai na Allãh ba, alhalin suna masu shaidawa kansu kafirci. Ayyukan waɗannan basu da amfaani kuma a wuta zasu dawwama.
- Sûrah A-Tawbah : 17.
Duk wanda ya mutu kan Shirka babba baza a yafe masa ba kuma za a haramta masa Aljannah kamar yanda Allãh Yace:
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِۦ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ
Lallai Allãh ba ya yafewa sanya masa kishiya a bautarshi, amma yana yafewa (duk) abunda yake koma bayan haka ga wanda ya so.
- Sûrah An-Nisã' : 48.
Kuma Allãh, Mafi Girma, Yace:
إِنَّهُۥ مَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِ ٱلْجَنَّةَ وَمَأْوَىٰهُ ٱلنَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍۢ
Lallai wanda ya sanya wa Allãh kishiya wajen bauta Allãh ya haramta mishi Aljannah kuma makomarsa wuta. Kuma ga azzalumai basuda mataimaka.
- Sûrah Al-Mã'idah : 72.
Ga wasu daga cikin misalan shirka babba;
1). Kira ga matattu (karkata addu’a garesu, roƙonsu)
2). Kira ga (roƙon) gumãkã.
3). Neman taimako daga gumaka ko matattu
4). Yin yankã ga gunki ko matacce.
✒ Bayanin Muhimman Darussa (ga kowane Musulmi) na Shaykh 'Abdul-'Azîz b. Bãz (رحمه الله).
✒ Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Darussalam Publishers, UK.