Addu’a Itace Ibaada


Manzon Allãh ‎(ﷺ) ya ce:

Addu'a itace ibaada 

[Sunan Abi Dawûd]

Shaykh Sãlih al-Fawzãn (حفظه الله تعالى) yace:

"Addu'a itace mafi girman nau'i na ibaada domin tana nuni ga ƙanƙantar da kai zuwa ga Allãh, cikakken buƙatuwar bawa ga Allãh, tattausar zuciya da kuma kwadayin abunda yake wurin Allãh, tsoron Shi, da kuma amincewar bawa da cewar shi mai rauni ne da tsananin buƙatuwa zuwa ga Allãh, yayin da shi kuma barin addu'a yana ishara ne ga girman kai, tattaurar zuciya, da kuma juya baya ga Allãh. Yin watsi da addu'a sababi ne na shiga wuta."



Daga ayyukan Shaykh Albãni (رحمه الله)  wanda Shaykh Muhammad Ibn Hassãn Ãli Shaykh ya taara // Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Fassarar turancin Ustãdh Rasheed ibn Estes Barbee.

Previous
Previous

Matsayin Tawhidi Ga Zukãta

Next
Next

Qaiʾdoji Huɗu [Darasin 5]