Falalar Tawhîdi da Ke Janyo Jin Daɗi A Rayuwar Duniya
Daga falalar Tawhidi da ke janyo Jin daɗi a rayuwar duniya da kuma lahira shi ne abunda Shaykh ya ambata a babin da ya gabaata na littafinshi kuma an taƙaita su a abunda zai biyo:
(1). Shi ne babban musababbin tsira daga damuwar duniya da lahira.
(2). Daga mafi girman faa'idojinshi shi ne katange mutum daga dawamma a gidan wuta dawwama ta har abada- idan akwai ko da kwayar zarra (ta Tawhidi) a cikin zuciyar.
(3). Idan ya kammalu a cikin zuciya yana hana shiga wuta gaba-daya.
(4). Yana gadarwa da ma'abocinshi cikakkiyar shiriya da cikakken aminci a rayuwar Duniya da Lahira.
(5). Shi ne hanya guda ta samun yardar Allâh da kuma sakamakonShi.
(6). Daga mafi girman falalarsa shi ne dukkanin ayyuka da zantuttuka na bayyane da na boye sun dogara akan karbuwarshi da kuma cikarshi, haka zalika matakin ladan ayyukan sun dogara akan Tawhidi.
(7). Yana gayyatowa bawa sauki wajen aiwata alheri da barin munanan ayyuka kuma yana tsame bawa daga bala'i. Saboda haka Duk wanda yayi gaskiya wajen imaninsa da Allâh da Tawhidi za a sanya ayyukan ɗa'a su zamanto masu sauki a wajenshi sanadiyar tsammaninsa na sakamakon Ubangijinsa da yardarsa. Haka zalika za'a sawwake masa ƙauracewa abubuwan da rai yake sha'awa na zunubi - saboda tsoron Fushin (Ubangijinsa) da azabarSa.
(8). Idan Tawhidi ya kammalu a zuciya; Allâh zai sanya ma'abocin Tawhidin ya so Imâni sai ya ƙawatã mishi (imanin) a zuciyarsa kuma ya sanyashi ya ƙyamaci kafirci da aikata sharri da saɓo kuma ya sanya shi cikin shiryayyu.
(9). Yana suakaka nauyin al'amura masu rudani akan bawa kuma yana janyo sauki a kowanne ƙunci. Domin haka gwargwadon kammaluwar Tawhidi da imanin bawa; ana fuskantar al'amura masu rudani da kuma halin ƙunci da farar zuciya da rai wanda yake a kwance kuma ya sallama ya yarda da ƙaddarar Allâh (mai kunshe da ƙunci).
(10). Yana warware bawa daga dukkanin bukatuwa zuwa ga bayi da ta'allaqa zuwa garesu da tsoronsu da sanya tsammani cikinsu da yin ayyuka saboda su. Wannan shi ne haƙiƙanin izza; kuma shi ne karamci cikakke.
(11). Idan Tawhidi ya cika kuma ya kammalu a zuciya kuma ya tabbatu cikakkiyar tabbata tare da iklasi kammalalle; wanan zai sanya mafi kankantar ayyukansa su zamto masu yawa; kuma a nunka ayyukansa da kalamansa ba tare da iyakancewa kuma ba tare da ƙayyadewa ba.
(12). Allâh yana azurta ma'abota Tawhidi da nasara a rayuwarnan ta hanyar karamci da mutunci da cimma shiriya kuma a dora su akan hanyar sauki da gyaruwar al'amura da dacewa a zantuttuka da ayyuka.
(13). Daga fa'idojinshi shi ne Allâh yana kautar da sharrin rayuwar Duniya da Lahira daga ma'abota Tawhidi - ma'abota imani. Haka zalika yana sabbaba musu rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali da natsuwa gareShi da natsuwa wajen ambatonShi.
(Duba: Al-Qawl As-Sadeed // Shaykh ʿAbdur-Rahmân b. Nâsir As-Sa'dî (Allâh ya jikan shi) // p.15-19)
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga WrightStreet Mosque.