Tafsir: Kai Kaɗai Muke Bautawa Kuma Daga WurinKa Kaɗai Muke Neman Taimako. Ash-Shaykh Ibn ʿUthaymîn

Sharhin Shaykh Muhammad b. Sãlih Al-ʿUthaymîn (r. 1421H)

"Kai kaɗai" ― إِيَّاكَ ― "Iyyaaka":

Wannan shi ne wanda aiki ya fada a kai (wato maf'ulun bihi) na kai tsaye, wanda ya zo kafin aiki (fi'ili) na'budu "muke bautawa". A nahawu, idan wanda aiki ya fada wa (maf'ulun bihi) na kai tsaye ya gabaaci aikin (fi'ilin) yana bayar da fa'idar taƙaitawa, sai ma'anar ta zamanto "Bama bautawa kowa ko komai faace Kai kaɗai."

"Muke buatawa" ― نَعۡبُدُ ― "Na'budu":

Muna ƙan-ƙan da kawunanmu zuwa gareka sallamawa cikakkiya. Ta hanyar wannan, zaka samu cewa muminai suna sanya mafi karamcin gaɓar jikinsu (wato fuskokinsu) a wurin da ƙafafuwansu (ke takawa) saboda khushu’i da ƙan-ƙan da kai zuwa ga Allãh (azza wa jal). Suna sujjada a ƙasa, suna turbude goshinsu da ƙasa. Wannan shi ne khushu’insu gaban Allãh. Dadin dadawa, idan da wani zai ce "Zan baka duniya da duk abunda ke cikin ta, kawai yi min sujjada sau daya." Bazaka taba samun muminai na gaskiya sun yarda da wannan ba saboda irin wannan ƙan-ƙan da kai ibaada ce da ake kebanta Allãh da ita shi kaɗai. Kalmar ibaada ta ƙunshi aiwatar da duk abunda Allãh yayi umarni da shi da ƙauracewa duk abunda yayi hani. Duk wanda bai bi wannan ba, baya aiwatar da abunda aka umarce shi kuma ba ya barin abunda aka haneshi bai zamanto bawa na gaskiya ba. Bawa shi ne wanda yake ɗa'a ga Wanda yake bautawa a abunda Ya shar’anta. Dan haka bauta tana lizimtawa 'yan-adam su aiwatar da duk abunda aka umarcesu da kuma barin duk abunda aka haramta musu. Amma aikata wannan ba zai yiwu ba faace se da agaji da taimakon Allãh. Domin haka ne Allãh (سبحانه وتعالى) yace…

"Kuma daga wurinka kaɗai muke neman taimako" ― وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ ― wa Iyyaaka nasta'een":

Ma'ana, "ba ma neman taimakon kowa a ibaada ko wani abu koma bayan haka." Wannan "neman taimakon" shi ne neman tallafi, da taimako, kuma Allâh (سبحانه وتعالى) ya haɗa tsakanin bauta (ibaada) da kuma neman tallafi ko tawakkali (dogaro akan Allâh) a wurare masu dama cikin Qur'ãni. Wannan ya kasance ne saboda ibaada (bauta) ba za ta taba tsayuwa ba face da taimakon Allâh, sallama al’amura gareShi da kuma dogaro akanShi.

Fa'idoji daga Sûrah Al-Fatiha, aya ta biyar (5):

(1) - Daga fa'idar wannan ayar shi ne tsarkake ibaada (iklasi wajen bauta), wanda na Allâh ne kaɗai, kamar yanda ya fadi, "Kai kaɗai muke bautawa." Wannan yana nuna cewa bautar nan Allâh kaɗai ake yiwa, saboda zuwan maf'ulun bihi na kai tsaye (Kai) kafin fi'ilin (muke bautawa) kamar yadda dokokin nahawu suka Shar'anta.

(2) - Wata fa'idar ita ce cewar neman taimako daga Allâh ake kaɗai sanadiyar jumlar, "kuma daga wurinKa kaɗai muke neman taimako". Haka zalika maf'ulun bihi na kai tsaye ya gabaaci fi’ilin wanda yake fa’idantar da takaitawa kamar yanda ya zo a farkon ayar. Bayan ambaton wannan, idan wani kuma ya tambaya; ta yaya neman taimako zai zamo daga Allâh zalla bayan ya zo a wani fadinSa cewar:

﴾وَتَعَاوَنُواْ عَلَى الْبرِّ وَالتَّقْوَى﴿

"Ku yi taimakekeniya wajen kyautatawa da Taqawâ"

[Sûrah Al-Mâidah : 2]

Ta yaya zamu fahimci waɗannan jumloli guda biyu bayan a wannan ayar Allâh ya tabbatar da neman taimako daga waninShi? Kuma Annabi ‎(ﷺ) yace:

"Taimakawa mutum ya hau dabbarshi, dora shi a kanta ko ɗaga mishi kayanshi (yayin da yana kanta) - duka wannan (tamkar) sadaka suke."

[al-Bukhaaree (no. 2891) da  Muslim (no. 1009) suka rawaito.]

Amsar wannan tambayar shi ne cewar neman taimako da tallafi nau’i biyu ne; neman taimako tare da sallama dukkanin al'amura zuwa ga wanda ka tambaya. Ka dogara gabakidaya akan Allâh kuma ka yarda cewa sakamakon ba zai zo daga ƙarfinka ko ikonka ba- wannan nau'in neman taimakon daga Allâh (azza wa jal) kaɗai akeyi. 

Nau'i na biyu shi ne neman taimako ta hanyar hadin gwiwa a wani abu da kake son ka cimma. Wannan nau'in ya halatta idan har wanda aka tambaya rayayye ne kuma yana da ikon aikata abunda ake tambayarshi. Wannan ba a kallonshi a matsayin nau'in ibaada. Wannan nau'in ne Allâh yayi magana akai yayin dayake fadi:

﴾وَتَعَاوَنُواْ عَلَى الْبرِّ وَالتَّقْوَى﴿

"Ku yi taimakekeniya wajen kyautatawa da Taqawâ"

[Sûrah Al-Mâidah : 2]

Idan aka kuma tambaya “Shin neman taimako daga halittu ya halatta a dukkanin lokuta da dukkan hali?”

Amsar ita ce, a'a. Neman taimakon halittu ya halatta ne kaɗai yayin da wanda ake tambaya ya zamanto yanacewa da cikakken ikon (aikata) abunda ake tambayarsa, idan ba haka ba neman taimakonsa bai halatta ba. Misalin wannan shi ne neman taimakon wanda ke cikin kabari wannan bai halatta ba hasali ma babbar shirka ne wannan (Hada Allâh da wani wajen bauta)! Wannan ya kasance saboda mutumin dayake cikin kabari bashida ikon taimakon kanshi ba ta yaya har zai taimaki wani?

Haka zalika, idan wani ya nemi taimakon wani mutum wanda ba ya tare da shi, kamar wani ya ƙudurce cewar wani daban a yankin gabas na duniya zai iya taimakonshi a wani abu a nashi yankin (wato yankin shi mai neman taimakon). Wannan shi ma Shirka ne babba domin ɗayan mutumin bashida ikon taimakonshi alhalin yana wata ƙasar.

Yanzu idan aka tambaya, "Shin ya halatta neman taimako daga halittu idan sharudan nan sun cika?" Amsar ita ce ya fi mutum ya gujewa tambayar taimakon kowa illa idan abun ya zamanto wajibi kokuma an sani cewa bayar da wannan taimako zai faranta wa mutumin rai. A wannan hali mutum zai iya neman taimakonsa don ya sa mishi farinciki. Kuma abunda za ka nemi taimakon wani cikinsa kar ya zamanto zunubi ne ko abunda aka haramta.

[Daga: The Fundamentals of Tafseer & Tafseer of Soorahs: al-Faatihah, al-Ikhlaas, al-Falaq da an-Naas Na Shaykh Muhammad ibn Saalih al-‘Uthaymeen, Tarbiyyah Bookstore Publishing]

Previous
Previous

Falalar Tawhîdi da Ke Janyo Jin Daɗi A Rayuwar Duniya

Next
Next

Tafsir: Kai Kaɗai Muke Bautawa Kuma Daga WurinKa Kaɗai Muke Neman Taimako. Ash-Shaykh As-Sa’di