Meyasa Allaah Ya Hallici Mutum Da AlJan?

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

﴾وَما خَلَقنَا السَّماواتِ وَالأَرضَ وَما بَينَهُما لاعِبينَ﴿

﴾ما خَلَقناهُما إِلّا بِالحَقِّ وَلكِنَّ أَكثَرَهُم لا يَعلَمونَ﴿

Kuma bamu hallici sammai da kassai da duk abunda ke cikinsu ba domin wãsa kawai; Bamu hallice su ba fãce saboda gaskiya (wãto mu gwada mu kuma jarrabci wadanda suke masu ɗā’a da kuma waɗanda suka kangare sannan mu sãkãwa masu ɗã’a kuma mu azabtar da waɗanda suka kangare) Sai dai mafi yawan su basu sani ba” — [Sūrah ad-Dukhān : 38-39]

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

وَما خَلَقنَا السَّماءَ وَالأَرضَ وَما بَينَهُما باطِلًا ذلِكَ ظَنُّ الَّذينَ كَفَروا فَوَيلٌ لِلَّذينَ كَفَروا مِنَ النّارِ

Kuma bamu hallici sammai da ƙasa ba da duk abunda yake cikinta ba taare da manufa ba! Wannan zato ne na waɗanda suka Kãfirce! —[Sūrah Ṣād : 27]

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

وَخَلَقَ اللَّهُ السَّماواتِ وَالأَرضَ بِالحَقِّ وَلِتُجزى كُلُّ نَفسٍ بِما كَسَبَت وَهُم لا يُظلَمونَ

Kuma Allâh ya hallici sammai da ƙasa da gaskiya, domin a saaka wa kowanne mutum da abunda ya aikata kuma ba za a zalunce su ba. — [Sūrah al-Jāthiyah:22]

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

وَما خَلَقتُ الجِنَّ وَالإِنسَ إِلّا لِيَعبُدونِ﴾ ﴿

Kuma ni (Allâh) ban hallici Aljanu da mutãne ba fãce don su bauta mun (Ni kaidai) — [Sūrah adh-Dhāriyāt:56]


Aʾlām As-Sunnah Al-Manshūrah - Na al-ʿAllāmah Ḥāfiẓ al-Ḥakamī - sh. 15

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial

Previous
Previous

Menene Ma’anar Ibãda?