Menene Ma’anar Ibãda?
﷽
العبادة اسم جامع لكلّ ما يُحِبّه اللهُ ويَرضَاه من الأقوالِ والأعمال الظّاهرة والباطِنة
Ibaada (Al-ʿIbādah) wani suna ne gamamme wanda ya ƙunshi dukkanin abunda Allāh ya ke so kuma ya yarda da Shi wanda ya kunshi furuci da ayyuka na bayyane da na ɓoye.
Ta yaaya zamu gane cewar ibaada mai soyuwa ce ga Allāh kuma yardaddiya ce awurin shi? Ana ganewa ne saboda Allāh ya turo manzanni kuma ya saukar da litattafai domin su umarce su da abunda Allāh yake so kuma ya yarda da shi; su kuma hane su daga abunda Allāh ya ke ƙi ya kuma tsaná. Ta hanyar haka ne hujjojin Allāh (Mafi Kammaluwa) suke tabbatuwa Kuma Hikimarsa (Mafi Kammaluwa) ta ke bayyana.
Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:
﴾رُّسُلًا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةٌۢ بَعْدَ ٱلرُّسُلِ ۚ﴿
Manzanni masu bushãrã da yin gargadi domin kar da mutãne su samu hujja akan Allāh bayan Manzanni — [Sūrah An-Nisā’:165]
Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:
﴾قُلْ إِن كُنتُمْ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِى يُحْبِبْكُمُ ٱللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ ۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ﴿
Ka ce (Ya Muhammadu wa Mutãne): Idan Kun kasance kuna (Haƙîƙanin) son Allâh toh ku bi ni (wãto ku amshi tawhīdī ku bi Qur’ãni da Sunnah), Allāh zai sõ ku ya kuma yãfe muku zunuban ku. Kuma Allâh mafi gãfara ne Mafi Rahama — [Sūrah Āl-ʿImrān:31]
Aʾlām As-Sunnah Al-Manshūrah - Na al-ʿAllāmah Ḥāfiẓ al-Ḥakamī - sh. 19-20
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial