Umarnin Farko Na Qur'âni
﷽
Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعْبُدُوا۟ رَبَّكُمُ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ وَٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ ❋ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ فِرَٰشًا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءً وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَخْرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزْقًا لَّكُمْ ۖ فَلَا تَجْعَلُوا۟ لِلَّهِ أَندَادًا وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ
Yaa ku mutane! Ku bautawa Ubangijinku (Allāh), Wanda ya halicce ku da Wanda suka gabace ku ko kun zama daga cikin masu Taqwá (Taqawa). Wanda ya halitta muku duniya a matsayin gurin hutu, da kuma sama a matsayin rumfa, kuma ya saukar da ruwa daga sama, kuma ya sa kayan itatuwa a matsayin abin ci. Don haka, kada ku yi wa Allāh kishiya bayan kun sani — [Sūrah al-Baqarah:21-22]
Fadin " Babu Mahalicci mafi chanchanta da a bauta masa sai Allāh " yana tilasta "korewa" da kuma "tabbatarwa", yana kore kowane abu da ake bautawa bayan Allāh saboda basu chanchanta da a bauta musu ba. Tauhidin addinin ya kafu ne akan wannan abubuwa biyu, kamar yadda Allāh ya fada cewar Ibrāhīm [عليه سلام] ya fadawa mutanen sa. Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:
وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦٓ إِنَّنِى بَرَآءٌ مِّمَّا تَعْبُدُونَ ❋ إِلَّا ٱلَّذِى فَطَرَنِى فَإِنَّهُۥ سَيَهْدِينِ
Kuma ku tuna lokacin da Ibrāhīm yace da mahaifin sa da kuma mutanen sa: "lallai, na barranta kaina daga abunda kuke bautawa; face shi (bana bautawa kowa face Allāh shi kadai) Wanda ya halicce ni, kuma lallai, shi zai shirye ni." — [Sūrah az-Zukhruf:26-27]
Wannan shi ne hanyar kowane ma'aiki da Allâh ya turo[ zuwa ga mutane]. Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:
وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِى كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولًا أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱجْتَنِبُوا۟ ٱلطَّـٰغُوتَ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنْهُم مَّنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ ٱلضَّلَـٰلَةُ ۚ فَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُكَذِّبِينَ
Mun aiko cikin kowacce al’umma manzo (yana mai Shelanta): Ku bautawa Allâh (Shi kaɗai) ku ƙauracewa (ko ku guje wa) taaghut (dukkanin abubuwan bauta na ƙarya, waato kar ku buatawa taaghut koma baya ga Allâh) — [Sūrah an-Naḥl:36]
﴾فَمَن يَكْفُرْ بِٱلطَّـٰغُوتِ وَيُؤْمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسْتَمْسَكَ بِٱلْعُرْوَةِ ٱلْوُثْقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَا﴿
Duk wanda ya kaafircewa taaghut ya yi imani da Allâh yayi riqo da urwatul wuthqa (igiya mai qarfi) wadda baza ta tsinke ba — [Sūrah al-Baqarah:256]
Duk wanda ya fadi cewar: “Babu abun bautaawa da cancanta sai Allāh” ya bayyana ‘yantuwar sa daga kowanne abun bauta koma baayan Allâh kuma ya wajabta wa kanshi (ko ta wajabta wa kanta) bautar Allāh (shi kaɗai). Wannan alkawari ne da mutum ya wajabta a kansa. [1]
Wajabci na ƙarshe shi ne Mutum ya mutu akan Tawḥīd (Tauhîdî);
﴾فَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسْلِمُونَ﴿
“Kar ku mutu faace kuna musulmai — [Sūrah al-Baqarah:132]
Saboda haka, wajibi ne a kanka ka bada matukar kulaawa ga al’amarin Tauhidi daga farko da kuma ƙarshen rayuwarka. [2]
[1] - Daga Muhaadaraat Fil Aqeedah Wad-Da’wah. 1/7-17. Na al-ʿAllāmah Shaykh Salih al-Fawzân - حفظه الله.
[2] - Rasaa'il Fil Aqeedah - Shaafi 55. Na ash-Shaykh Hammâd Al-Ansârî
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial