Menene Ma’anar لا اله الا الله - Lâ Ilâha Ilâ Allâh ?

Ma’anarsa: Shi ne: kore bautar komai koma bayan Allāh, da kuma tabbatar da cewa Allāh ɗaya ne ba shi da abokin tarayya a cikin bautarsa, kamar yadda bashida abokin tarayyah wajen mulkinSa (kan komai).

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

﴾ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلْبَـٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْكَبِيرُ﴿

Hakan saboda Allāh shi ne Gaskiya (Ubangiji guda ga dukkan halittu (da ya cancanci bauta) wanda bayida kishiyoyi), kuma waɗanda su (mushirikai) suke kira koma bayan shi bâtil (ɓata, ƙarya) ne, kuma hakika Allāh shi ne Mafi Ɗaukaka, Mafi Girma — [Sūrah al-Ḥajj:62]


Aʾlām As-Sunnah Al-Manshūrah - Na al-ʿAllāmah Ḥāfiẓ al-Ḥakamī - sh. 37

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial

Previous
Previous

Umarnin Farko Na Qur'âni

Next
Next

Menene Ma'anar Musulunci?