A Ina Allãh Ya Ke?


Daga Mu'ãwiyah bin Al-Hakam As-Salamî wanda yace: 

Na kasance ina da baiwa wadda ta ke kula da tumaki na a yankin Uhud da Al-Jawãniyyah. Ta fita wata rana sai kyarkeci ya ɗauke ɗaya daga cikin tumakin. Ni ɗan adam ne daga ‘ya’yan adam, ina yin fushi kamar yanda suke fushi. Saboda haka sai na mare ta, yayin da na je wurin Manzon Allāh ‎(ﷺ), sai ya bawa al'amarin muhimmanci matuka. Na ce: "Ya Manzon Allâh, shin ba zan 'yanta ta ba kuwa?"

Yace: "kawo mun ita." Sai na kawo ta wurinshi. Yace mata: "a ina Allâh yake?" Tace: "yana sama." Yace: "wanene ni?" Tace: "kai ne Manzon Allâh." Sai yace: "'yanta ta yanzu, domin lallai ita Mumina ce."

Daga: Muslim ne ya rawaito, Babin Masallatai (537). Abû Dâwûd, Babin Sallah  (930), Babin Imâni da Nudhoor (3282). Mâlik a  al-Muwatta (1511). Ahmad (27718, 27720) daga hadisin Mu'âwiyah. Ahmad ya rawaito (7846) da Abû Dâwûd (3284) daga hadisin Abû Hurayrah (رضي الله عنه).

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar Turancin Abû Khadeejah  ʿAbdul-Wâhid 'Alam.
Previous
Previous

Samun Yaƙini Game da Allãh