Samun Yaƙini Game da Allãh

🖌️ Al-ʿAllãmah Ash-Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. ʿAbdillãh b. Bãz (رحــمه الله):

Al-Yaqîn [Yaƙini] yana nufin (mutum) ya zamanto mai imãni da Allãh akan tabbataccen ƙuduri da yaƙini; mutum ya yi Imãni cewar Allãh shi ne Ubangijinsa, Guda, na gaskiya, da yake bautawa; da kuma cewar babu wanda ya cancanci bauta koma bayanshi; Cewar Shi ne mahaliccin komai; kuma cewar Shi Kamalalle ne a zaatinsa, da ayyukansa, da cewar Shi, Mafi tsarkaka, wajibi ne a bauta Mishi shi kaɗai kuma a kaɗaita Shi da bauta.

Kuma ya wajaba akan Mu'mini ya kiyaye sharrin harshen shi daga faɗin abubuwan da zasu rage (wato su aibanta martabar) Ubangijinsa, ko kore siffofinsa, ko raina abunda ya umarceshi da Shi.

Mumini ya sani da yaƙini cewar Shi-Mafi tsarki da ɗaukaka-ne Kaɗai wanda ya cancanci a bauta miShi; cewa shi ne Ubangijin Ɗukkanin halittu; Shi ne Al-Khallāq [mai yawan-halitta ko kuma mai yin halitta a kowanne lokaci], Al-'Alîm [Masanin komai]; cewar Shi Kaɗai ne wanda ya cancanci bauta; kuma babu wani Ubangiji koma bayanShi kuma babu wani mahalicci koma bayanShi; babu wani koma bayanShi da ya cancanci a bautamasa, Mafi tsarki da ɗaukaka.

Kuma ya kudurce da yaƙini cewar zai tara mutane ranar tashin Al-ƙiyãma; ya Saaka musu ayyukansu- da alheri idan alheri (suka aikata), da kuma sharri idan sharri (suka aikata).

Ya sani da yaqini cewar Allãh, Mafi tsarki da ɗaukaka, zai cika al-ƙawarurrukansa, ya sanya muminai a Aljannah kamar yanda yayi musu al-ƙawari, ya kuma sanya kafirai a wuta kamar yanda yayi musu al-ƙawari, Mafi tsarki da ɗaukaka.

Haka zalika, duk abunda Allãh da manzonsa ya fada a al-Qur'ãni ko a cikin ingantattun Hadisai, mumini yayi imani dasu ya gasgata su kuma ba shi da shakku akan wannan.

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar Turancin Mikaîl ibn Mahboon Ariff.


Previous
Previous

Kurakurai Cikin Aqeeda - Musanta (ƙaryata) ʿUluww na Allâh da Istiwa - Shaykh ʿAdul-ʿAzîz bn Bâz

Next
Next

A Ina Allãh Ya Ke?