Bayani Daga Kwamitin Manyan Malamai Game da Ikhwân-ul-Muslimîn (wato: ‘Yan Braza)


Dukkan yabo ya tabbata ga Allâh, Ubangijin dukanin halittu, kuma Salaati da sallama su tabbata ga bawanSa da manzonSa wanda aka bawa amanar isar da sakonSa kuma Mafi falalar halittunSa, Annabinmu, Shugabanmu, Muhammad b. ʿAbdullâh. Amincin Allāh ya tabbata ga iyalensa Sahabbansa da duk waɗanda suka bi tafarkinsa da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:

Haƙiƙa Allâh (تَبَارَكَ وتَعَالى) yayi umarni da haɗin kai akan gaskiya kuma ya haramta rarrabuwa da saɓani . Shi (سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى) yace:


إِنَّ الَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمْ وَكَانُواْ شِيَعًا لَّسْتَ مِنْهُمْ فِي شَيْءٍ إِنَّمَا أَمْرُهُمْ إِلَى اللّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَفْعَلُونَ

"Haƙiƙa wanda suka rarrabu a addininsu suka kasu zuwa ƙungiyoyi kai (Ya Muhammad ﷺ) babu ruwanka da su. Al'amarinsu na ga Allāh kuma Shi ne zai gaya musu abunda suka kasance suna aikatawa." [Sûrah Al-An’âm, 159]

Haka zalika ya umarci bayinSa da bin mikakkiyar hanya kuma ya hanesu da bin hanyoyin dasuka sabawa gaskiya.

Shi (سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى) yace:


وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلاَ تَتَّبِعُواْ السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَن سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

"Kuma Lallai wannan hanyata ce mikakkiya ku bi ta, kuma kar da ku bi wasu hanyoyi koma bayanta domin lallai za su raba ku daga hanyarShi. Wannan yayi muku wasiyya da shi domin ku zamanto masu Taqawa." [Sûrah Al-An’âm, 153]

Saboda haka, bin mikakkiyar hanya zai cimmu ne kaɗai ta hanyar riko da Littafin Allâh (عَزّ وجَلّ) da Sunnar ManzonSa ‎(ﷺ). Haka zalika ingantattun hadisai suna kafa hujjar cewa hanyoyin da Allāh yayi hani da bin su su ne kungiyoyi da ɗarikoki dasuka yi hannun riga da gaskiya. An rawaito daga ingantaccen hadisin ʿAbdullâh b. Mas'ûd (رضي الله عنه) inda yace:

Manzon Allâh (ﷺ) ya zana layi da hannunshi yace: "wannan ce hanyar Allâh mikakkiya." Sai yayi zane a damanshi da hagunshi yace: "wannan ne sauran hanyoyi. Babu wata hanya acikinsu face akwai sheɗani yana kira zuwa gareta."

Sannan ya karanta ayar:

وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلاَ تَتَّبِعُواْ السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَن سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

"Kuma Lallai wannan hanyata ce mikakkiya ku bi ta, kuma kar da ku bi wasu hanyoyi koma bayanta domin lallai za su raba ku daga hanyarShi. Wannan yayi muku wasiyya da shi domin ku zamanto masu Taqawa." [Surah Al-An’âm, 153]

- Imâm Ahmad ya rawaito.

Sahabin nan mai falala, ʿAbdullâh b. ʿAbbâs (رضي الله عنها) ya ambata game da fadin Allâh (تَبَارَكَ وتَعَالى): "Ku bi ta, kuma kar da ku bi wasu hanyoyi koma bayanta domin lallai za su raba ku daga hanyarShi." Da fadinShi (Allâh):

عِيسَى أَنْ أَقِيمُوا الدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُوا فِيهِ

"Cewar ku tsayar da addini kuma kar da ku rarrabu aciki.” [Sûrah Ash-Shûrâ, 13]

Akwai sauran surori a Qur’āni masu shige da waɗannan. [Ibn ʿAbbâs] yace: "Allâh ya umarci muminai da Jama'ah (wato yin riko ga uwar jikin Musulman da suke tare da gaskiya), kuma ya haramta su daga rarrabuwa da kasuwa, kuma ya sanar da su cewar bai halaka waɗanda suka zo gabaninsu ba face saboda gardama da rikici a addinin Allâh."

Haka zalika riko da Littafin Allâh (عَزّ وجَلّ) da sunnar Manzo (ﷺ) shi ne hanyar da zai sa Allâh ya yarda (da mu), kuma shi ne asali ta hanyar wanda hadin-kai da zaman lafiya zai auku. Dadin-dadawa, shi ne hanyar da take kariya daga dukan sharri da ibtila'i.

Allâh yace:

وَاعْتَصِمُواْ بِحَبْلِ اللّهِ جَمِيعًا وَلاَ تَفَرَّقُواْ وَاذْكُرُواْ نِعْمَةَ اللّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنتُمْ أَعْدَاء فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُم بِنِعْمَتِهِ إِخْوَانًا وَكُنتُمْ عَلَىَ شَفَا حُفْرَةٍ مِّنَ النَّارِ فَأَنقَذَكُم مِّنْهَا كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ

"Kuma kuyi riko dukkaninku zuwa ga igiyar Allâh kuma kar da ku rarrabu a tsakaninku, ku tuna ni'imar Allâh a kanku, domin kun kasance maƙiyan juna amma ya hada zukatanku tare, sai kuka kasance - da ni'imarShi - 'yan-uwa (a Musulunci), kuma kun kasance a bakin wuta sai ya cece ku daga ita. Haka Allâh yake bayyana ayoyinshi (hujjoji, ayoyi, alamomi da sauransu) domin ku kasance shiryayyu." [Sûrah Âl-ʿImrân, 103]

Don haka daga abunda ya gabaata ya kamata a sani cewa duk abunda zai yi tasiri (mara kyau) akan zaman lafiya da hadin-kai game da shuwagabannin musulmi, kamar yaɗa miyagun shubuhohi da (ɓatattun) akidu, ko kafa ƙungiyoyi inda ake yin muba’aya (wato bay’ah), ake tsarin ƙungiya da sauran su, haramun ne kamar yanda Littafi da Sunnah suka kafa hujja.

A sahun gaban waɗannan ƙungoyoyi da muke gargadi daga bin su ita ce ƙungiyar "Muslim Brotherhood" (Al-Ikhwân Al-Muslimîn, 'Yan Braza). Ɓatacciyar ƙungiya ce wadda aka kafa ta bisa rikici da shuwagabannin musulmi da yin tawaye akan hukuma (ta Musulunci).

Suna tayar da tarzoma a kasashe da yawa, suna rikita zaman lafiya (wanda yake tsakanin 'yan ƙasa) suna kiran kasashen musulinci 'Jâhili Al'umma' (wato al'ummomin jahiliyyah).

Sannan kuma, tun kafa wannan kungiya, ba a taba ganin ta bawa ingatacciyar aqidar musulunci kulawa ba, kuma bata taba bawa sauran fannonin ilimi da suka shafi Littafi da Sunnah kulawa ba. Manufar ta kaɗai shi ne cimma mulki da shugabanci. Wannan ne ya saka tarihin wannan kungiya cike yake da sharri da rikici. ɗadin dadawa kuma wannan ƙungiya ita ta haifi kungiyoyin 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayi waɗanda suka shuka fasadi tsakanin mutane da kuma cikin kasashe. Wannan abu ne sananne kuma a fili, kamar rikici da ta'addancin da ake aikatawa a fadin duniya.

Domin haka, daga abunda ya gabaata, ya bayyana cewa “Muslim Brotherhood (‘Yan Braza)” kungiya ce ta ‘yan ta’adda kuma ba ta wakiltar Aqidar Musulunci, tana kawai bin ajandar ta ne na ɓangarancin siyasa da suka saɓawa shiriyar addininmu mai tsarki. Suna ɓoye kansu bayan addini a lokaci ɗaya kuma suna aikata abunda ya saba mishi na daga rarrabuwa,tayar da rikici, tashe-tashen hankali da ta'addanci.

Daga karshe, wajibi ne akan kowane mutum ya yi hattara da wannan kungiya, kar da ya ƙulla ƙawance da ita, ko ya jajanta mata.

Muna rokon Allâh ya kare mu daga dukkan sharri da ibtila' mummuna.

Amincin Allâh da albarkaSa su tabbata ga Annabi Muhammad da iyalensa da duka mabiyansa.

Sauke.


Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Abû Suhayl Anwar Wright.

2 / Rajab / 1444 هــ.

24/ January / 2023.


Previous
Previous

Bikin Ranar Masoya (Valentine’s Day)

Next
Next

Yin Musharaka Da Kafirai Wajen Bikin Kirismeti (Christmas).