Bikin Ranar Masoya (Valentine’s Day)


Matambayi:

Bikin ranar masoya (Valentine’s Day) ya zama ruwan dare a kwanan nan, musamman tsakanin dalibai mata. Bikin kristoci ne kuma suna bikin shi ta hanyar saka jajayen tufafi wanda ya kunshi jajayen kaya da jan takalma, kuma ta hanyar musayar jajayen furanni(wato fulawa). Za muso bayani daga [Shaykh] mai daraja akan hukuncin bikin ire-iren wadannan abubuwan. Kuma, menene nasihar ku ga musulmai game da ire-iren wadannan abubuwa? Allah ya kiyaye ku kuma ya kula da al’amuran ku.


Shaykh Muhammad b. Sãlih Al-ʿUthaymin:

Bikin ranar masoya [Valentine's Day] baya halatta daga fuskoki da dama. Da farko, biki ne wanda ba ya cikin al'adar (Musulmai) wanda bashi da tushe a Shari'ah. Na biyu, yana karfafa so irin wanda ya ke wuce gona da iri da sha’awa (haramtacciya). Na uku, yana iza mutum zuwa shagaltar da zuciyarsa da kaskantattun al'amura marasa amfani waɗanda kuma suka sabawa shiriyar Magabata na Kwarai (Salaf As-Salih), Allâh ya yarda dasu.

Don haka baya halatta a soma wani abu a wannan rana a matsayin abun biki, ko ta hanyar bayar da abinci, abun sha ko kaya, musayar kyaututtuka ko wani abu.

Musulmi dole ya samu izza daga addininsa kuma kar ya zamanto mabiyin mutane, wanda yake bin kowa da kowa. Ina rokon Allâh mafi Daukaka da ya tsare Musulmai daga dukkanin fitintinu, na zahiri da boye, da ya kuma kiyaye mu ta hanyar daukan nauyin al’amuranmu da kai mu ga samun nasara.


Daga: Majmu Fatawa Ash-Shaykh Ibn ʿUthaymin (16/199)

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Daar us Sunnah (UK).


18 / Rajab / 1444 هــ.

9/ February / 2023.

English

Previous
Previous

Ranar April Fool’s

Next
Next

Bayani Daga Kwamitin Manyan Malamai Game da Ikhwân-ul-Muslimîn (wato: ‘Yan Braza)