Ranar April Fool’s
﷽
Shaykh Ṣāliḥ bn Fawzān Al-Fawzān (حفظه الله):
Tambaya:
Ranar ‘April Fool’s’ ta shahara tsakanin wasu mutane a kasar waje - a kasashen da ba na Musulunci ba - ranar daya ga watan afirilu, kuma wasu Musulmai suna kwaikwayon su a hakan ta yanda suke daukan cewa ya halatta suyi karya a wannan ranar…Menene ra’ayinku game da wannan aqida da kwaikwayo?
Amsa:
Karya ba ta halatta kwatakwata a kowane lokaci, kuma ba ya halatta a biyewa kuma a kwaikwayi kafirai a wannan (al’amarin) da wannin shi saboda fadin Annabi ﷺ (Duk wanda ya kwaikwayi wasu mutane yana daga cikinsu)
Daga: Fatawar Shaykh Ṣāliḥ Al-Fawzān Majallatul Shaqā’iq # 32 a watan Safar
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Abū Mu’ādh Taqweem