Hukuncin Kan Cin Abincin Kafirai Da Suka Girka Don Bukukuwansu - Al-'Allāmah Ṣāliḥ Al-Fawzān


Mai Tambaya:

Shin ya halarta cin abincin kafirai da suka girka don bukukuwansu idan ya kasance mutum zaici bayan kwana biyu da bukukuwa?

Shaykh Ṣāliḥ b. Fawzān al-Fawzān:

A'a! Duk abin da aka shirya (abinci ko abin sha) don bukukuwan arna ba za'a ci komai daga cikinsa ba saboda acikin cin sa akwai nuna yarda garesu. Don haka ba za'a ci daga yankansu ba, hakanan girke girkensu, hakanan ya'yan itace da zasu zo dasu don murna don yin hakan yarda dasu.


Next
Next

Hukuncin Karanta Sūrah Al-Fātihah Lokacin Kwangilar Aure