Hukuncin Karanta Sūrah Al-Fātihah Lokacin Kwangilar Aure


An tambayi Shaykh Muḥammad ibn Ṣāliḥ Al-ʿUthaymīn (Allāh ya jikan shi) game da hukuncin karanta Al-Fātihah lokacin kwangilar aure, kuma an fadu cewa da ya faru da waensu mutane sun maye gurbin kwangilar gabaki daya, don haka sai suce “Na karanta Al-Fātihah akan ta” kuma da niyyar hakan anyi aure, ya amsa:

Wannan bai halatta ba, maimakon haka Bidi’ah ce. Karanta Al-Fātihah ko wanin shi daga takamaimman Suwar (wt: Surorin Al’Qurani) ba za a karanta su ba faace a wuraren da aka halatta su. In ka karanta shi a wanin wurin da ba daidai ba - a matsayin aikin ibaadah - a na daukan ta a matsayin Bidi’ah. Kuma lallai mun ga yawancin mutane na karanta Al-Fātihah a ko wane buki, har ya kai muna jin waɗanda suke cewa “ku karanta Al-Fātihah” akan mamaci kuma akan wan da wancan, da dukkanin wadannan [suna] daga kirkiran al’amura da mugun aiki.

Don haka, Al-Fātihah kuma banda shi daga Suwar ba a karantawa a ko wane hali da ake ciki,  ko wuri ko lokaci faace in wannan (karantawa a wannan halin da ake ciki, wuri ko lokaci) an halatta bisa ga Littafin Allāh (wt: Al’Qurani) ko Sunnan ManzonSa (ﷺ) kuma in ba haka ba, toh Bidi’ah ce kuma wanda ya aikata ta ana zargin sa.

Daga: Fatāwá Nūr ʿAlā Darb na Shaykh Al-ʿUthaymīn (10/95)

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Salafi Center na Manchester (UK)

Previous
Previous

Hukuncin Kan Cin Abincin Kafirai Da Suka Girka Don Bukukuwansu - Al-'Allāmah Ṣāliḥ Al-Fawzān

Next
Next

Ranar April Fool’s