Ma’anar Dimokuradiyya [Democracy] da Tarihin Ta
﷽
Shaykh Muhammad Amãn Al-Jãmi - Allãh ya jikan shi - :
Muna kira zuwa ga Allãh akan basira kuma ba ma tuntube ko rikita [al'amura], kuma rashin basira shine (sakamakon) abunda ya bayyana daga wadansu marubutan da [masu amfani da] hankali agaban [komai, hatta nassi] na wannan zamanin, musamman a alamarin da ya alakanci da Al-Hãkamiyah wurin da suke rikita al'amarin kundin tsarin mulki [wato constitution].
Al-Amarin shariah yana bukatar ayi mishi karatu na musamman (a karance shi karatu mai zaman kansa) kuma ba ko wane mai ilimi, ko Daliban Ilimi ne ke cin nasara kuma ya zama mai kira a wannan fannin ba. Misali, mutane dayawa suna kira ga Dimokaradiyya [democracy], suna tunanin ma'anar Dimokuradiyya shi ne adalci kuma wannan babban kuskure ne. Kamar yadda kalmar Dimokaradiyya kanta bakuwar [kalma] ce, (kamar haka) bakon al’amari ne wanda ba daga Musulunci yake ba, hasali ma tsarin kafiran turawa ne.
Ma'anar Dimokuradiyya shi ne "Shugabantar mutane ta hanyar mutane", kuma tushen wannan ya kasance lokacin (zamanin da) Kristocin yamma suka zauna ɗan wani lokaci cikin tãkura, kuma karkashin zaluncin sarakunansu, shugabanni da cocina [churches]. Sakamakon haka sai sukayi tawaye - kamar tawayen yan'uwan mu a Falasdinu yadda suka yi wa Yahudawa.
Su kayi tawaye kuma suka kin bin umarnin sarakunan su, shuwagabanni da mulkin cocinansu. Suka tsere wa wannan zaluncin, amma ga me suka tsere zuwa? Sun gudu daga shugabancin mutum zuwa shugabancin mutum, kamar mutumin dake neman taimako daga kasar da rana ta gasa ne daga [zafin] wuta. Sai suka yanke shawarar cewa [adadin] gamagarin Jama'ah zata shugabanci kanta kuma don haka, [zasu] samu jin dadin cikakken yanci.
Wannan yana nufi, basu gudu zuwa (basu nemi mafaka wurin) Allãh da aiwatar da dokokin Allãh ba, a madadin hakan sun gudu daga zalunci zuwa aiwatar da nasu azzalumin dokokin na mutane, saboda dan-adam - kasancewar yadda yake daga dan adam, ya tattara a cikin sa zalunci da jahilci faace wanda Allãh ya ceta daga samun waɗannan siffofin.
Wannan dimokaradiyyar , da tushen ta, siffofin ta da asalin ta basu zo daga Musulmai ba, saboda ta kore imanin mutum ga Allãh, tunda daga imani da Allãh shi ne yin imani da shariar Allãh, da hukuncin Allãh. Domin haka Dimokuradiyya ba daga Addinin Allãh bane, balle adalci, ba daga adalci ba ce, a maimakon haka [kawai] hanyar [aiwatarwa da] ayyuka da kuma [sanadin kawo] rudani ne, saboda ta hada gabaki daya abunda ake kira yancin kowane mutum.
Kuma game da wannan yancin addini (bisa ga Dimokuradiyya) mutum zai iya rayuwa na wani lokaci akan wani addini (a matsayin) bayahude, kirista ko musulmi kuma sannan ya chanja zuwa ko wane addini da ya zaba, ma’ana basu da hukuncin Ridda.
[Ma'anar] Dimokuradiyya shi ne yancin yin magana, yancin yin addini, yancin yin tafiya, dukkannin yanci da yake kunshe da rudani faace yancin Musulunci da ya takaita da koyarwar Musulunci. Wannan itace Dimokuradiyya…
Kiran zuwa ga Dimokuradiyya daga waɗannan marubuta Musulmai da siffantawarsu dasukayi mata [Dimokuradiyya] na adalci, (sanadin) rashin basira ne, tunda kira zuwa ga rayuwar majalisar na nufin bin fristoci da monks [ma'abota bauta sosai daga mutanen littafi]] saboda bin dokokin mutane ne. Yan takara (da suke gasa wajen samun) kuri'a da samun shugaba wanda yake shar'anta dokoki don far'anta wa al'umma kuma basa la'akari da ko waɗannan dokokin sun yadda da Musulunci ko suna saba mishi, kuma wannan na kore Tawheedi na Hukuncin Allãh.
ٱتَّخَذُوٓا۟ أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَـٰنَهُمْ أَرْبَابًۭا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلْمَسِيحَ ٱبْنَ مَرْيَمَ وَمَآ أُمِرُوٓا۟ إِلَّا لِيَعْبُدُوٓا۟ إِلَـٰهًۭا وَٰحِدًۭا ۖ لَّآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ عَمَّا يُشْرِكُونَ
"Su [yahudawa da kristoci] sun dauki malaman su da ruhbanahum [ma'abota bauta sosai daga mutanen littafi] din su, su zama iyayen-gijinsu koma bayan Allãh [ta hanyar yi musu biyayya a abubuwa da suka halasta musu ko haramta musu bisa ga nasu son ra'ayin ba tare da Allãh ya umurce su ba)" [Surat At-Tawbah : 31]
Babu bambanci tsakanin waɗannan mutanen majalisa da waɗancan fristoci da monks [ma’abota bauta daga mutanen littafi ] [waɗanda Allãh ya ambata] saboda dukka wannan ya fada cikin hukunci da wata dokar da ba dokar Allãh ba.
Hakannan daga abunda yake kuskure shi ne bayarwa mutane sunan "Ma'abota doka [mutanen dake kirkiro doka]" A Musulunci babu Ma'abota-Doka [mutanen da ke kirkiro doka], hasali ma a Musulunci ba a samun dokoki [na mutane] gaba ki daya. Mai bayar da doka shi ne Allãh, (dokar) da aka isar daga Allãh ta [hanyar] Manzon Allãh (ﷺ). Domin haka, Allãh ya shar'anta kuma Manzo (ﷺ) ya isar kuma dokokin Allãh ana samun su a Littafin Shi da kuma Sunnar Manzon Sa (ﷺ).
Kira zuwa ga abunda suke kira dimokuradiyya [sunayi] saboda rashin basira ne. Kuskure ne kuma rikita [al'amari] dangane da lamarin shari'ah. Yana kore Tawheedin Sharee'ar Allah, wannan shiyasa da'awar mu ta barranta daga da’awa zuwa ga waɗannan alkawuran dake kore Musulunci saboda wannan daga rashin basira ne.
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fasarrar turancin DaarusSunnah (UK).