Raddi Akan Shubuhan Mutanen Bidi'a - "Ku Dauki Gaskiyar Ku Bar Karya"


Raddi akan shubuha da Mutanen Bidi'a suke yadawa waɗanda suke cewa: "Ku dauki gaskiyar ku bar karyar daga cikin maganganu da litattafan Mutanen Bidi'a!"

Shaykh Khâlid Dahwî Adh-Dhufayrî [‏حفظه الله]yayi raddi akan wannan shubuhar a fadinshi :

Kuma daga cikin hanyar kubuta daga fitina shi ne nisantar Mutanen Bidi'a, da yin takatsantsan da su da kuma yin gargadi a game dasu. Wannan asali ne na Salafiyyah da ma'abota ilimi suka ambata kuma Qur'ani yayi nuni gareshi (wannan asalin) da Sunnah dakuma maganganun Magabata na Kwarai: Sahabbai, mabiyansu da kuma wasun su. Ma'abota ilimi sun hadu akan barin Mutanen Bidi'ah da kuma kaurace musu kuma wannan ijma'in an rawaito shi daga malamai dayawa.

Duk sun yarda akan cewar a kauracewa Mutanen Bidi'ah da kuma barin karanta litattafansu ko kallon litattafan, saidai wanda yake so yayi raddi a garesu [1]. Su kuma sauran mutane kada su karanta litattafansu ko saurarar wani abu face daga ma'abota ilimi kuma su kauracewa masu bin zuciya (Ahlul Ahwa); su saurari Mutanen Sunnah kuma su kauracewa Mutanen Bidi'ah kuma bamu fadin wannan batacciyar kuma sabuwar dokar: "ku dauki gaskiya ku bar abinda ba gaskiyaba".

Babu shakka cewar an umarce mu da mu dauki gaskiya kuma mu bar wanda yake ba gaskiyaba amma ba'a umarce mu da mu dauki gaskiya daga mutanen bidi'ah da masu son zuciya ba! Muna karbar gaskiyane daga ingantacciyar hanya kuma muna dauka daga gurinda babu shakku ko wata Bidi'ah!

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Fassarar turancin Abû Abdir-Rahman Mehdi Al-Maghribee tare da taimakon Abû-l-Husayn (Yûsuf Mcnulty Al-Irlandee) da Abû Tasneem (Mushaf Al-Banghalee).

Bayanin Kula


[1] - Daga mai fassara; wannan na malaman Ahlul Sunnah ne kuma Malamai sun yi bayaanin sharudan sa.

Previous
Previous

Ma’anar Dimokuradiyya [Democracy] da Tarihin Ta

Next
Next

Bidi’o’i Suna da Haɗari