Mala’iku Suna Nemawa Masu Azumi Yafiya - Al-‘Allāmah Ibn ‘Uthyamīn


Shaykh Muḥammad b. Ṣāliḥ Al-ʿUthaymīn - رحمه الله - Ya Ce:

Daga cikin ɗabi’un watan ramadana shi ne kasancewar mala’iku suna nemawa masu azumi yafiya har sai sun karya azumin su. Kuma Mala’iku baayi ne masu karamci a wurin Allāh,

لَّا يَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ

Ba sa saɓawa Allāh abunda ya umarce su da shi, kuma suna aikata abunda aka umarce su. [Sūrah At-Taḥrīm:6]

Domin haka sun fi cancanta Allāh ya amshi addu’ar su da suke yi wa masu azumi; yayin da kuma ya basu dama. Sannan ‘Istighfār’ shi ne neman yaafiya, wanda shi ne suturce zunubai a duniya da lahira, da yin afuwa game da su, kuma shi (istighfaari) ne mafi ƙololuwar abunda ake nema, kuma mafi tsadar manufa.


Majālis Shahr Ramaḍān sh 108

Fassarar: AMMAN CIRCLE Editorial


Previous
Previous

Idan Ban Sauke Qur’āni A Watan Ramadana Ba Shin Ina Da Zunubi? - Imām Ibn ‘Uthaymīn

Next
Next

Niyyar Azumi - Shaykh Al-Islām Ibn Taymiyyah