Jingina Kai Ga Tafarkin Magabaata (Salaf)


Tambaya:

Wasu mutane ba sa kiran kansu da Ahlus-Sunnah wal-Jama’ah (waɗanda suke riko da Sunnah da kuma Jama’ar Musulmai) suna za’amin cewa dukkan mutane suna yin hakan. Suna cewa ya fi dacewa musulmai su jingina kansu ga Salaf (Magabaata na Kwarai). Shin wannan daidai ne?

Amsa:

Salaf su ne Ahlus-Sunnah wal-Jama'ah. Domin haka ya halatta ga mutum ya jingana kanshi zuwa Salaf. Yin hakan daidai ne, don ɗaya yake da kiran kanka Ahlus-Sunnah wal-Jama'ah, wanda yayi imani da Allâh da ranar ƙarshe, kuma mai bin Sahâbah (Sahabbai Annabi). Yayin da mutum ya jona kanshi zuwa ga Salaf, ya jona kanshi ne zuwa ga ma'abota gaskiya, ba ma'abota ɓata ko karya ba. Domin haka dole ne ya jajirce wajen zama mai gaskiya. 


Majmû' Al-Fataawa Ibn Bâz (28/50)

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Tashar Abû Bilaal Nahim ibn Abd Al-Majîd (Majmoo' al-Fataawa).




Previous
Previous

Menene Salafiyya? Kuma Ga Me Take Kira Zuwa (Muqadimah)

Next
Next

Bidi’ah Tafi Soyuwa Wurin Iblîs