Salaf Sune Ma'abota Sunnah
﷽
Ash-Shaykh ʿAbdul-ʿAzîz b. Bãz (رحمه الله)
Tambaya:
Shaykh mai daraja! Wannan mai tambaya ne ta hanyar shirin[nan] yana tambaya : Shin akwai bambanci tsakanin fadin mu : "wannan cewar Salaf ne ko wannan cewar Ahlus-Sunnah ne?
Amsa Daga Shaykh ʿAbdul-ʿAziz b. Baz:
Ma'anar daya ce. Salaf sune Ma'abota Sunnah kuma sune : Sahabbai Allãh ya kara musu yarda gaba ki daya, da waɗanda suka bi su da kyautatawa.
Ana dangana musu ita kalmar a [matsayin] : Salafus Sãlih (Magabata Na Kwarai) kuma ana ce musu : Ahlul-Sunnah wal Jamã'ah. Idan yana nufin hakan, babu matsala ko kadan. Shi sunan yana nuni ne zuwa ga abu daya; Ahlul-Sunnah wal Jamã'ah, As-Salaf As-Sãlih.
Kuma manufar ma'anar sa a wurin ma'abota Sunnah ya nuni ga: Sahabban Annabi (ﷺ), sallama da albarka agare su da waɗanda suka bi su a kyautatawa a ʿAqîdah, zance da ayyuka.Na'am.
Mai gabatarwa :
Allãh yasaka muku [da alkhairi].
Fassaran AMMAN CIRCLE Editorial.