Koyi Aqeeda A Wata Biyar
Shaykh Muhammad Ammãn Al-Jãmî (رحمه الله) yace:
Lallai wanda ya fadi hakan mutum ne wanda bashi da komai a zuciyar sa [na Aqeeda daidai] kuma yayi nisa daga ingantacciyar Aqeedah. “Menene matsalar waɗanda suke koyan Aqeedah, Aqeedah, Aqeedah tsawon rayuwarsu gabaki dayanta? Wata biyar ko shekara biyar ya isa (koyon) Aqeedah!" Wanda aka hana shi abu bazai iya bayar da shi ba!” Idan bashi da komai, al’amari mai nauyi. Muna rokon Allah ya albarkace mu da kyauta daga gareShi.
Wannan mutumin bashi da lafiya, ina ma ace yana da masaniya game da cutar shi da jahilcin shi. Al-Aqeedah wajibi ne a koda yaushe cigaba da [koyanta ] da yin riko da ita har sai ka hadu da Ubangijinka. Al'amarin su abun ban mamaki ne! Ba sa cewa meyasa kullum kuke koyan Kitãbu Salãh [Littafin Sallah], Kitãbu Tahãra [Littafin Tsarki] da Kitãbu Zakãh [Littafin Zakah], meyasa sai baza ku koya a shekara biyu ko uku ba (kaɗai) shikenan ku gama.
Basa juya wa komai baya sai Aqeedah, sababin wannan shi ne wata cuta a cikin zukatan su. Wannan Aqeedar imani ce, imani yana kafuwa ne kaɗai yayin da babu cuta a zuciya, amma zuciyar da ba tada lafiya tana ƙin Aqeedah, bata son umurni da abu mai kyau da hani da sharri kuma tana samun rashin natsuwa game da abu kyau.
Wannan Aqeedar imani ce, ko kace wannan Aqeedar da muke koya wani sashe ne daga manya-manyan sassan imani kaman yanda muka ambata. Mun yi bayani cewar imani ya kunshi furucin harshe, aikin gabbai da kuma aikin zuciya.
Kuma Aqeedar da muke koya aiki ne daga ayyukan zuciya. Domin haka koyan aqeeda a dukkannin mataki, har ga gamagarin mutane, ba wanda yake da uzurin [rashin] neman ilimin Aqeedah.
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turncin Salafi Centre of Manchester (UK)