Asulan Tawhidi - 1 - Tawhidi Shi Ne Tushen Addini


Dukkan godiya ta tabbata ga Allâh ( سبحانه وتعالى) shi kadai, muna gode Masa, kuma muna neman taimakon Sa da gafararSa. Muna neman tsari da Allâh daga sharrin kawunanmu da kuma Sharrin munaanan ayyukanmu. Duk Wanda Allâh ya shiryar babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allâh ya batar, babu mai shiryar da shi. Na shaida cewa babu abun da ya cancanta a bautamasa da gaskiya sai Allâh, shi kadai ba tare da abokin tarayya ba, kuma Muhammad (ﷺ) bawansa ne kuma ma'aikinsa ne.

Bayan Haka:

Mafi gaskiyar zance shi ne kalaaman Allâh kuma mafi kyaawun hanya ita ce hanyar Muhammad (ﷺ). Mafi munin al'amari sune ƙirƙirarrun al'amura, kuma kowanne ƙirƙirarren al'amari Bidi'ah ne kuma kowacce Bidi'ah ɓata ce kuma kowanne ɓata yana cikin wuta.

DARASI NA FARKO: TAWHIDI SHI NE TUSHEN ADDINI

An wajabta mana fahimtar muhimmancin Tawhidi da azabar da za'a yiwa waɗanda suka juya mishi baaya- wannan shi ne Mafi mahimmancin al'amari da aka ambata a cikin Qur'āni.

Ma'abota Tawhidi su ne mutanen Aljannah. Amma ma'abota Shirka waɗanda suka bautawa wani koma baayan Allâh an haramta musu aljannah kuma makomarsu ita ce wuta.

Hakan ya kasance ne saboda ma'abota Tawhidi sun bautawa Allâh shi kaɗai - ma'ana sun yi gaskiya kuma sun tsarkake bautarsu ga abun bauta daya bisa ga cancanta (a larabci: Al-Ilah) - basu karkata kowane sashe na bautarsu zuwa ga wanin Allâh ba, ba zuwa ga Annabawa ba, ko Salihai, ko taurari ko Malaa'iku ko bishoyoyi ko Salihan Mutane, basu riki kowa a matsayin tsaka-tsaki tsakaninsu da Ubangijinsu ba, suna kira gareShi ne kai tsaye wajen sallah da addu'a, walau a haalin sauki ko kunci.

Mutanen Tawhidi suna bautawa Allâh, abun bauta daya bisa ga cancanta, kamar yanda Annabawa da Manzanni sukayi cikin dukkanin zamani, har zuwa bin su ga Manzo na Karshe, Muhammad (ﷺ) Bayan aikosa, an rufe annabta, ta yanda ya zamanto dukkanin addini ana daukarsa ne daga wahayin da aka saukar masa. Dayawa daga litattafan farko sun samu canji daga hannun kawunnan kiristoci da rabbaniyoon- saboda haka sai Allâh ya turo Annabin ƙarshe (ﷺ) da wahayi (Al-Qur'âni da Sunnah) wanda ya shafe dukkan wahayuyyukan dasuka gabaata.

Domin haka ma'abota Tawhidi suna bautawa Allâh shi kaɗai Kamar yanda Manzon Allâh (ﷺ) a aikata.

Ma'abota Tauhidi basu takaitu a ƙasa daya ba, ko a yanki daya, ko a ƙabila daya, ko launin fata daya- a'a, duk wanda ya bautawa Allâh yayi watsi da dukkanin nau'in shirka kuma yabi Manzon Allâh (ﷺ) toh mutumin Aljannah ne. Takan iya yiwuwa a azabtar da wasu daga cikin mutanen Tawhidi sanadiyar zunubansu da basu kai Shirka ba, amma azabar baza ta zamanto dawwamammiya ba, kuma a karshe za a shigar dasu Aljannah.

Kowane ma'abocin tawhīdi sai ya shaida kaɗaituwar Allâh da kuma manzoncin Muhammad. Dangane da shahadar tawhīdi, ita ce "Lâ ilāha illallâh" (Babu abun bautawa da cancanta sai Allâh) - ma'anar babu Ubangiji, wani abun bauta da ya cancanci bauta a gaskiya faace Allâh. wannan Shahadar ta ƙunshi abubuwa guda biyu:


Na Farko: Kore karkarta bauta zuwa ga wani abu koma bayan Allâh (Mafi ɗaukaka) saboda babu wani abu da ya cancanci bautarmu.


Na Biyu: Tabbatar da bautar gaskiya zuwa ga Allâh shi kaɗai - da wannan ne ibada tsarkakakkiya ta ke cimmuwa, ta hanyar wannan babbar shahada, kuma da ita ne mutum yake shiga Musulunci. Ta hanyar wannan Shahaadar mutum yake samun aminci da kariya dangane da rayuwarshi dukiyarshi da mutuncinshi Duniya - kuma ya ke cimma tsirã a Laahira.

Daga sharudan karbar wannan shahadar tawhidin shi ne mutum dole sai ya ambace ta da yaƙîni da kuma ilimi, da son ranshi ba tare da an tursasa shi ba- kuma ana bukatarshi da samun yakini da tabbatuwa cewa babu abun bautawa a gaskiya, wanda ya cancanci bautarshi (koma bayan Allâh).

Wasu na iya tambaya: "menene yake damunku, kuna bawa Tauhidi matukar kula kuma kuna yawaita magana akanshi, kuma mu daga abunda muke gani daga gareku ba kwa damuwa da sauran al’amuran Musulmai a lokacin nan, waɗannan Musulman da ake kashewa ko ake kora daga ƙasashensu, ko makiyansu suke bibiyarsu, daga kafirai da sauransu."


Sai mu ce a matsayin jawabi ga wannan (kuma shiriya daga Allâh ta ke): Tawhidi shi ne tushe bisa wanda addini tsayayye ya ginu a kai.

Idan mukayi tadabburin Qur'âni, wannan babban littafi wanda yake cike da al'ajabi muke karanta shi a wannan watan na Ramadana darensa da ranakunsa, zamu samu cewa Qur'âni yayi bayanin al'amarin Tawhidi ne gaba dayanshi- har ya zamanto cewa babu wata surah daga surorin Al-Qur'âni faace tana bayanin Al'amarin Tawhidi wanda shi ne bautar Allâh shi kaɗai, da kaɗaita Allâh a abunda haƙƙinShi ne shi kaɗai, ta Hanyar SunayenShi, SifofinShi, BautarShi (wadda bayinsa zasu yi zuwa gareshi) da AyyukanShi.

Qur'âni haka zalika ya haramta Duk abunda ya ƙalubalanci Tawhidi, ko wace surah tana da wani nau'i na ambaton Tawhidi cikinta.

Tawhidi shi ne asalin manufar aiko manzanni (عليهم السلام) daga farkonsu zuwa ƙarshensu. Allâh Mafi ɗaukaka ya cewa Annabi (ﷺ):


وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ

Kuma bamu tura gabaaninka manzo ba faace sai mun yi mishi wahayi cewa 'babu abun bautawa bisa cancanta faace ni, domin haka ku bauta min'. [Sûrah Al-Anbiyâ' : 25]

Kuma Allâh ya sanar da 'yan Adam cewa dukannin Annabawa suna cewa mutanensu:


لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ إِنِّيَ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Kuma tabbas mun aika Nuhu zuwa ga mutanenshi ya ce ‘ya ku mutane na ku bautawa Allāh baku da wani abun bauta koma bayanShi, tabbas ina ji muku tsoron azabar rana mai girma’. [Sûrah A'râf : 59]

An aiko annabi Muhammad (ﷺ) domin tabbatar da tauhidi tabbatarwa cikakkiya ya kuma hani mutane daga sanyawa Allâh kishiyoyi, ko da abun da ya kasance shirka babba ne ko karama. Allâh ya faɗi game da kanShi:


رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَاعْبُدْهُ وَاصْطَبِرْ لِعِبَادَتِهِ هَلْ تَعْلَمُ لَهُ سَمِيًّا

"Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abunda ke tsakinsu, domin haka ka bauta miShi kuma ka dawwama ka yi hakuri wajen bautarShi, shin ka san wani makamancinShi?" [Sûrah Maryam: 65]

Wannan ayar ta kunshi nau'i uku na Tawhidi:

Na Farko - shi ne RububiyyarSa (Ubangijintakar Allâh) cikin fadin sa: Ubangijin sammai da kasa da abunda yake tsakaninsu."

Na Biyu - Shi ne bautarShi (Uluhiyyar Allâh): cikin fadin sa; "Domin haka ka bauta miShi kuma ka dawwama ka kuma yi hakuri wajen bautarShi."

Na Uku - shi ne sunayenShi da SiffofinShi cikin fadinShi: "Shin ka san wani makamancinSa?" Wanda yake tabbatar da cewa Allâh yana da sunaye da Siffofin da suka keɓanta da Shi, ta yanda babu abunda yake shige da shi, Mafi Girma da ɗaukaka.


Imâm Ibnul Qayyim (Allâh yayi mishi rahama wanda ya rasu 752A.H) ya ambata cikin Madârij As-Sâlikîn (Mujalladi na 3) Al'amarin Qur'âni da kuma yanda yake jaddada Tawhidi. Ibnul Qayyim yace dukkanin Qur'âni yana magana ne game da Tawhidi. Qur'âni ya kunshi bayaani game da Sunaye da Siffofin Allâh, RububiyyarShi da AyyukanShi, wanda ake kira Tawhîd Al-ʿIlmi, wato ilimi da Siffofin da Suka Shafi Allâh shi kaɗai- wannan ya kunshi kaɗaituwar Allâh a RububiyyarShi da SunayenShi da SiffofinShi.


Qur'âni yayi umarni da bautar Allâh shi kaɗai, ba tare da kishiyoyi ba, kuma yana hani ga shirka. Wannan shi ake kira tawhidin ayyuka da ad-du'a (Al-Tawhîd Al-'Amalî At-Talabi) wato mutum ya sanya ayyukan bautarshi su zamanto na Allâh shi kaɗai, kuma ba ya neman kowa da addu'arsa, neman taimakonsa, neman mafaka, neman agaji da sauransu. Wannan shi muke kira Tawhîdin ʿUlûhiyyah wanda shi ne kaɗaita Allâh ta fuskar kasancewarShi abun bauta ɗaya da ya cancanci bauta, Shi kaɗai. Kuma ba ma sanyawa Allâh kishiya wajen bauta, ana kuma kiran wannan da Tawhîd Al-ʿIbâdah.


Al-Qur'âni yana umarni da biyayya ga Allâh (Mafi ɗaukaka) da ManzonSa (ﷺ), kuma Qur'âni yana yin hani daga saɓawa Allâh da manzonSa. Wannan al'amarin biyayya ga Allâh da ManzonSa da gujewa saɓawa Allâh da manzonSa yana daga cikin haƙƙoƙin Tawhidi. Kuma yana daga cikin kammaluwar Tawhīdin mutum da cikarsa.

Sakamakon wanda yayi aiki bisa Tawhidi shi ne Al-Jannah, yalwa, farin ciki, jin dadi da izza- wannan shi ne abunda Allâh yayi alƙawari ga wanda ya bauta miShi Shi kaɗai. Kuma sakamakon wadanda suka gafala daga Tawhidi sukayi watsi da shi shi ne Allâh zai azabtar dasu, ya ƙasƙantar da su, ya kunyatasu, kuma Allâh zai shigar dasu wuta su dawwama cikinta har abada.

Saboda haka munga cewar dukkanin Qur'âni yana magana ne kan Tawhidi. Idan da zaka yi nazari a surorin da aka saukar a makka, zaka samu cewa ayoyin makka da aka saukarwa da Manzon Allâh a farko farkon manzancinsa, wanda ya kunshi shekara goma sha uku (13) daga lokacin da ya karbi annabta yana mai shekaru arba'in (40), da karashen zamansa a Makka har ya kai shekara hamsin-da-uku (53), zaka samu cewa akasarin ayoyin suna magana ne akan Tawhidi- abubuwan da suka shafi gyaran aƙidar mutum ta hanyar bautar Allâh shi kaɗai, da kuma kushewar da Allâh yayiwa bautar gumaka, da sauran abubuwan bauta koma bayanShi.

Manzon Allâh (ﷺ) ya rayu a Makkah tsawon shekara goma sha uku, yana kira zuwa ga Tawhidi yana yin hani daga Shirka (hada Allâh da wani a bauta). Saboda haka kaso mai tsoka na daga wajibai kamar su zakkah, azumi, Hajji, Hijabi, Tufafin Musulunci, Haramcin Shan Giya, Cãcã, da sauran al'amuran Halâl da Harâm-waɗannan dokokin da hukunce hukuncen ba a saukar da su ba sai bayan hijira zuwa Madînah.

Banda salloli biyar na rana, waɗanda aka wajabta su a Makkah daren Mi'râji yayin da aka dauki Manzon Allâh (ﷺ) domin tafiyar Isrâ' da Mi'râj -wato tafiyar nan ta dare da zuwa sammai. Saboda haka wajabta salla ya faru ne kafin hijira ta ɗauki lokaci da kadan, amma mafiya yawan dokoki da hukunce hukuncen Shari'a ba a saukar da su ba sai bayan hijira zuwa Madînah.

Ita dai Makkah, an fi bayarwa ƙarfafa imanin Muminai kulawa, Kiran mutane ga bautar Allâh, bayyana ɓata da hasarar da ke cikin bautar gumaka da sauransu daga cikin abubuwan da mutane suka kasance suna yi. Allâh (wanda Ya barranta daga dukkanin tawaya, Mafi ɗaukaka) ya haramta dukkanin wannan- wannan shi ne abunda aka muhimmanta a Makkah, bautar Allâh shi kaɗai. Wannan ya ci gaba a Madînah bayan hijira tare kuma da sauran hukunce-hukunce da dokoki na bauta.


Ustâdh Abû Khadeejah ne ya rubuta.

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial.

10 / Jumâdâ al-Âkhirah / 1444 هــ.

3/ January/ 2023.



Previous
Previous

Asulan Tauhidi - 2 - Ina Zamu Fara?

Next
Next

Koyi Aqeeda A Wata Biyar