Menene Ma'anar Musulunci?

الإستِسلَامُ لله باالتَوحيد والإنقياد له بالطاعة والخلوص من الشرك

Musulunci shi ne mika wuya ga Allâh da Tauhidi (i.e imani da kadaita Shi a chikin bauta da kadaita shi a RubûbiyyarSa da sunayensa da siffofin Sa); da kuma sallamawa tare da biyayya gare Shi, da kuma ‘yanta kai daga shirka [wato barrantã daga yi masa shirka a cikin bauta, da kuma cikin RubûbiyyarSa da SunayenSa da SifofinSa].

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِّمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ وَٱتَّبَعَ مِلَّةَ إِبْرَٰهِيمَ حَنِيفًا ۗ وَٱتَّخَذَ ٱللَّهُ إِبْرَٰهِيمَ خَلِيلًا

Kuma wãnene ya fi fifiko a addini sama ga wanda ya sallama fuskarsa (shi kanshi) zuwa ga Allāh (wãto ya bi addinin Allâh na Tauhîdî) - [Sūrah an-Nisā' : 125]

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

وَمَن يُسْلِمْ وَجْهَهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ ٱسْتَمْسَكَ بِٱلْعُرْوَةِ ٱلْوُثْقَىٰ ۗ وَإِلَى ٱللَّهِ عَـٰقِبَةُ ٱلْأُمُورِ

Kuma duk wanda ya sallama fuskarsa ga Allāh, (wato mai bin addinin Allāh na Tauhidi), ya bauta wa Allāh (Shi kadai) yana mai tsarkake imani da kadaitar RububiyyarSa, da kadaitar da bautarSa, da kadaita sunayenSa da siffofinSa. Alhali shi Muhsin ne (mai kyautatawa wato yana yin aikin kwarai gaba daya don Allāh ba tare da riya ba ko neman yabo ko shahara da sauransu kuma ya aikata su bisa Sunnar Manzon Allāh Muḥammad), to ya yi riko da Al-ʿUrwah Al-Wuthqá [La ilaha ill-Allah (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allāh)].” - [Sūrah Luqmān : 22]

Allāh, Mafi Ɗaukakã, ya ce:

﴾ فَإِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ فَلَهُۥٓ أَسْلِمُوا۟ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُخْبِتِينَ﴿

Kuma abin bautãwarku abin bautawa ne Guda (Allāh), sabõda haka ku sallama Masa (a Musulunci). Kuma (Ya Muhammad) ka yi bushara ga Mukhbitin (waɗanda suka yi biyayya ga Allah da ƙanƙan da kai daga cikin muminai na gaskiya).” - [Sūrah Ḥajj: 34]

Aʾlām As-Sunnah Al-Manshūrah - Na al-ʿAllāmah Ḥāfiẓ al-Ḥakamī - sh. 37

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial

Previous
Previous

Menene Ma’anar لا اله الا الله - Lâ Ilâha Ilâ Allâh ?

Next
Next

Menene Ma’anar Ibãda?