Tafsir: Kai Kaɗai Muke Bautawa Kuma Daga WurinKa Kaɗai Muke Neman Taimako. Ash-Shaykh As-Sa’di

Sharhin Shaykh ʿAbdur-Rahmân bin Nâsir as-Sa'dî (r. 1376H):

FadinShi “kai kaɗai muke bautawa kuma daga wurinKa kaɗai muke neman taimako.” wato Muna kebance Ka da bauta da neman taimako tunda gabaatar da wanda aiki ya fada akai na iyakance aikin (gareshi). Shi (wannan iyakancewar) yana tabbatar da waɗannan siffofin kuma yana kore su daga saura. Kamar yana cewa ne, "muna bauta maka kuma ba ma bautawa wani koma bayanKa, muna neman taimakonKa kuma ba ma neman taimakon wani koma bayanKa."

An ambaci bauta kafin neman taimako ta fuskar gabaatar da gama-gari kaafin keɓantacce, da kuma bawa haƙƙin Allâh muhimmanci kafin haƙƙin bawa. Ibaada suna ne gamamme da ya kunshi dukkanin abunda Allâh ya ke so kuma ya yarda da shi na daga ayyuka da furici sawa'an zahiri ne ko a ɓoye. Isti'ânah (neman taimako) shi ne dogaro akan Allâh, Mafi ɗaukaka, wajen cimma amfani da kore cuta tare da cikakken ƙuduri cewa Yana da iko akan hakan.

Aiwatar da bautar Allâh da neman taimakonShi hanya ce da take kaiwa zuwa ga farin ciki dawwamamme da kuma tsira daga dukkanin sharri. Babu hanyar tsirã face da tsayar da waɗannan abubuwa biyu. Ibaada tana zama ibaada ne yayin da ta zamanto an ɗaukota daga Manzon Allâh ‎(ﷺ) kuma da niyyar neman fuskar Allâh. Saboda haka ta hanyar al'amuran nan biyu abu yake zama bauta (ibaada). An ambaci Isti'ânah (neman taimako) bayan ibaada duk da cewa yana ƙunshe ciki, saboda bawa yana da bukatar neman taimakon Allâh, Mafi Ɗaukaka, a dukkanin ayyukansa na bauta. Idan Allâh bai taimake shi ba ba zai iya cimma abunda yake muradi na bin umarni da kaurace wa hani ba. 

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga The Fundamentals of Tafseer & Tafseer na Soorahs: al-Faatihah, al-Ikhlaas, al-Falaq da an-Naas (wallafawar) Shaykh Muhammad ibn Saalih al-‘Uthaymeen, Tarbiyyah Bookstore Publishing.

5 / Jumâdâ al-Âkhirah / 1444 هــ.

29/ December / 2022.

Previous
Previous

Tafsir: Kai Kaɗai Muke Bautawa Kuma Daga WurinKa Kaɗai Muke Neman Taimako. Ash-Shaykh Ibn ʿUthaymîn

Next
Next

Asulan Tauhidi - 2 - Ina Zamu Fara?