Asulan Tauhidi - 2 - Ina Zamu Fara?

Mun ambata a darasi na farko cewar Sakon Annabin Allâh ‎(ﷺ) shi ne, a kan gaba, kira zuwa ga Tawhidi - da kuma cewar a zaman Makkah, wanda yake tsawon shekaru Sha uku, Allâh Mafi ɗaukaka ya umarci Manzon Allâh (‎ﷺ) da kira zuwa ga Tawhidi.

Mafi akasarin Surorin Qur'âni, (Surorin Makkah) da aka saukar wa da Annabi ‎(ﷺ) kafin hijirarsa zuwa Madinah suna kewaye ne da al'amarin Tawhidi wato wajabcin bautawa Allâh shi kaɗai- wanda ya ke nuna matukar muhimmancin wannan. Amma, game da sauran wajibai da suka shafi ayyukan ibada na zahiri, ba a saukar da su ba har sai da Tawhidi ya kafu kuma ya tabbatu a cikin zukata, kuma ingantaccen imani, da ingantacciyar aƙida  suka kafu.

Wannan ya kasance ne saboda ayyukan ibada na zahiri bazasu kasance sun inganta ba face da ingataccen Tawhidi. Ayyukan ibada na zahiri ba za su ginu akan komai ba face Tawhidi kuma Al-Qur'âni ya bayyana cewa al'amari na farko da Manzon Allâh (ﷺ) ya kira zuwa kafin komai shi ne kiransa zuwa ga bautar Allâh shi kaɗai. Wannan shi ne kiran kaɗaita Allâh da Manzon Allâh yayi, kira zuwa ga Tawhidi. 

Saboda wannan ne Allâh ya aiko Annabawa da Manzanni kamar yanda Allâh ya fadi:

وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولاً أَنِ اعْبُدُواْ اللّهَ وَاجْتَنِبُواْ الطَّاغُوتَ

Mun tura ga kowacce Al'umma manzo yana mai kiransu zuwa ga bautar Allâh da kauracewa abubuwan bauta na ƙarya. (Sûrah An-Nahl:36)

Da kuma fadin shi Mafi ɗaukaka:

وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ

Kuma ba mu aika gabaaninka (ya Muhammad) annabi ba faace sai da muka yi mishi wahayi cewa "babu abun bautawa da gaskiya sai Ni (Allâh) domin haka ku bauta min"(Sûrah Anbiya: 25)

Kuma kowanne Annabi sai da yace da mutanenshi:

وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ

Ya ku mutanena ku bautawa Allâh ba ku da abun bauta koma bayanShi. [Sûrah Al-A'râf:65]

Wannan yana nuna muhimmancin al'amarin Tawhidi. Wannan yana ishara ga cewar (Tawhidi) shi ne kira da kuma manufar turo dukkanin annabawa. Sun fara da'awarsu da kira zuwa ga bautar Allâh shi kaɗai. Kuma wannan shi ne. Tafarkin duk wanda suka bi manzanni a kowane zamani, lokaci da kowane wuri- waɗanda suke kira zuwa ga gyaran Al'ummah. 

Ustâdh Abû Khadeejah ne ya rubuta.

Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial.

11 / Jumâdâ al-Âkhirah / 1444 هــ.

4 / January/ 2023.

Previous
Previous

Tafsir: Kai Kaɗai Muke Bautawa Kuma Daga WurinKa Kaɗai Muke Neman Taimako. Ash-Shaykh As-Sa’di

Next
Next

Asulan Tawhidi - 1 - Tawhidi Shi Ne Tushen Addini