Bacci Da Rana A Ramaḍān
﷽
Shaykh Muḥammad b. Ṣāliḥ Al-‘Uthaymīn (رحمه الله) ya ce:
Dayawan mutane suna zama ido biyu cikin daren Ramadana. Wasun su suna tafiyar da gaba daya daren a abubuwa marasa amfani. Wasu suna tafiyar da duka darensu a aikata zunubi. Sanadiyar haka sai su karar da wannan rana a bacci. Wannan ba dai-dai ne ba. Ya kamata mutum ya yi amfani da ranar shi a yin zikiri, karatun Qur’āni, yi wa Allāh biyayya da kusantar Shi.
Daga: Fatāwá Arkan al-Islām sh. 480
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Dr. Mūsá Shaleem Mohammed.